Ni bako ne a wannan shafi in Allah zan ba da ra'ayina a kan bunciken da nayi domin duk mukaru baki daya. Na gode Allah ya saka da alkairi.

BIKIN HAUSAWA NA DA DA NA YANZU

gyara sashe

GABATARWA Idan muka ce jiya, muna nufin zamanin da aka fito, watau   “Zamanin da”. Idan kuma muka ce yau, muna nufin zamanin da muke ciki, watau “Zamanin yanzu”. Dangane da wannan yanayi na ga ya dace in yi wani tsokaci game da al' adunmu, da kuma ire-iren wasu bakin al'adun da suka cusu cikin namu da muke da su da. Sannan kuma yaya yanayin al'adunmu suke aq yau, da kuma al'ummar baki daya. Hausawa al'umma ce wadanda ke da al'adun da suka gada kaka kakanni, kuma mafi yawa al'adun kyawawa ne, amma sabili da zuwan da Turawa suka yi a kasarmu; suka yada al'adunsu ga al'ummar Hauswa har suka yi tasirin cikin zukatansu, sai su Hausawa suka dauki wasu al'adun Turawa suka cusa su a cikin nasu, musamman al'adun sha anin aure.         Ta bangaren haka ne al'adun Hausawa suka cakude suka koma 'yan anshn shatan al'adun Turawa. Watau duk wani   abu da Nasara ya kawo idan har ba a yi amfani da shi ba, to babu burgewa cikin wannan aure. Dangane da wannan ne, na ga ya dace in jawo hankalin 'yan'uwanmu mata, da ma maza baki-daya don mu dawo daga rakiyar bakin al'adu, mu koma a harkokin da muka gada tun Fil-azil dama “Yaro rike ungulunka shamuwa bakuwa ce”. Saboda duk al'ummar da ba ta rike al'adunta da muhimmanci ba, za ta sami wahaloli wajen bunkasarta. Don haka, al'ummar Hausawa idan son su sami bunkasa, wajibi ne su rike al'adunsu, su kuma kawar da wadanda ba nasu ba. Ina fatan wannan jawo hankali da zan yi, zai taimaka wa jama'a musamman Hausawa wajen bayar da haske dangane da irin abubuwan   da suka kamata a lura da su wajen dawo da martabar al'adun Hausawa.         MA'ANAR AL'ADA Ita wannan kalma ta al'ada, kalmar Larabci ce. Hausawa sun aro ta ne, kamar yadda suka aro sauran kalmomi. Ma'anarta, halin rayuwa; ko abin da aka saba wanda al'umma ta amince da shi. Masana a karni na ashirin sun bayyanar da al'ada da abubuwan da al'umma ke amfani da su, kamar su fasalin gine- ginensu da suturu da kuma yanayin huldarsu.              Kowace al'umma tana da tata al' ada wadda ta sa bamban da ta wata. Haka kuma fasalin rayuwar kowace   al' umma bai zama daya Wadanda suka hada da Bukukuwan suna, aure da shagulgula da akan yi a lokotai daban- daban na rayuwar yau da kullum.   Misali irin yadda Hausawa ke tafiyar da sha anin bukukuwansu ya bambanta da yadda Turawa ke tafiyar da nasu.   AURE A ZAMANIN DA         Dangane da yanayin aure a zamanin da, abu ne mai muhimmanci, ba kamar yanzu ba. A da saurayi bai fara neman yarinya aure, ba tare da sanin iyaye ba. sai iyaye sun sa da shi ta hanyar irin dawauniya da hiima da yake aiwatarwa tsakaninsa da abban yarinya, ko yayunta ko kannenta. A zamanin da abu na farko da ke gudana tsakanin saurayi da budurwa shi ne “Toshi”. Toshi kuwa abu ne mai muhimmancin gaske. watau kyautatawa tsakanin mai so, da kuma iyayen yarinya. Wannan kyautatawa ta fuskance bangarori da dama, ta fuskar sha'anin noma ne, ko kasuwanci ko hidimomin aikin gida ne da sauransu. A zamanin da idan saurayi ya ga yarinya; idan har yana son ta, to ta fannin harkokin gidansu zai nuna. Ko dai idan lokacin damina ne zai gaya wa abokansa ne su yi gungu-gungu su je gonar mahaifin yarinyar nan duk su nome ta. Idan yarinya ta fita ko da aikinta aka yi zai rinka bin ta, ba tare da ta sani ba. Haka zai rinka zagayawa a kai-a kai. Idan yarinyar ta fito sai ya bi ta. Haka dai zuwa! Idan kunyarsa ba mai yawa ba ce sai ya ce mata 'yan mata ina magana ne. Idan har ba mai kunya ba ce da yawa, takan tsaya; idan kuwa tana da kunya sosai; sai ta kara saurin shigewa gida. Ta haka ne har irin hidimominsa zai sanya shi har a gane wannan na son wance, ba kamar yanzu ba.            AL'ADUJ NEMAN AURE A DA Al'adun aure a da su ne:   1. Toshi 2. Kame 3. Kyauta   TOSHI Toshi abu ne da ake aiwatarwa tsakanin mai so da kuma iyayen yarinya. Toshi yakan kara sanya karfi wurin neman aure, domin ta haka ne akan gane cewa mutum da gaske yake yi, wanda shi zai ba shi damar iyayen yarinya su tabbatar da cewa yana cikin masu neman 'yarsu.   KAME Mame abu ne da ke faruwa tsakanin iyayen yaro da yarinya, idan har akwai abota, ko zumunci. Kame zai kara karfafa musu wannan. Wannan kame iyayen yaro yaro kan yi shi da zarar aka haifi yarinya. Uwar yaro, ko uba yakan buda baki ya ce na yi wa dana wane kamen 'yar nan. Idan da amincewa sai abin ya dore har akai ga aure.   KYAUTA Ita kuma kyauta takan faru ne a wani lokaci tsakanin mai gida da yaron gida. Akan yi kyauta ne sakamakon sanin yanayin yaro mai kirki ne da kuma sanin ya-kamata da ganin girmar na gaba da shi. Da irin haka ne za ka ga cewa uban gidan zai ce wa yaron na ba ka wance, zan taimaka maka da sadaki.           AL'ADUN NEMAN AURE A ZAMANIN YANZU         Al'adun namen aure a wannan zamani su ne:   1.      Haduwa Wurin Aure                   2.      A kan Hanya Ko Waya   HADUWA WURIN AURE   Akasarin yawan auren yanzu yakan faru ne a cikin wurin wani aure. Saurayi da budurwa kan hadu wajen wani aure ba tare da wani ya san wani ba, sai su shirya   kan su, daga karshe sai a je wurin iyaye.   A KAN HANYA KO WAYA Da yawa yanzu a kan hanya aure kan hadu har ma a kai da yin aure.   Ko ma ta waya ba tare da wani ya ga wani ba, har a yi zurfi wurin soyayya, daga nan sai aure ya bayyana nan take.   AL'ADUN NA NEMAN AURE         Akwai wasu al'adu da Bahaushe kan yi wajen neman aurensa, wadannan al'adu su ne kamar haka:   NEMAN AURE Mai nema yana tare da samu, inji masu iya magana. Aure bai yiyuwa ba tare da an name shi ba. Neman aure a zamani da, harka ce ta iyaye, saurayi da budurwa. Wani lokaci tun yara na goye ake daukar alkawarin hada su, kuma tun daga wannan lokacin iyayen na namiji za su rika yi wa iyayen yarinya kyauta, ko kuma toshi. Amma ko a da akan yi auren soyayya, wanda saurayi da budurwa ne za su hadu a dandali har su so juna, kafin iyayensu su sani. Idan iyayen sun goyi bayan a yi, to ba wani ka-ce-ka-ce na-ce-na-ce sai shiga nema sosai.   TABBATARWA Tabbatarwa Ita ce alkawarin da iyayen yarinya sukan yi ga manema, cewa wanda aka nema wa, shi ne zai aure ta. Muddin an tabbatar a kan, bukaci sauran manema da su janye. Iyaye yarinya sukan tambaye ta, ta fadi saurayin da take so daga cikin manemanta.         Akan sha wahala, kafin a sami amsa daga yarinyar, domin rashin kunya ne ga Hausawa fadin sunan mijinsu. Daga karshe za ta fadi wanda take so, amma ba sunan za ta fadi ba, iyayenta ne za su rika zana sunayen manemanta, ita kuma ta rika ce musu a'a, ko ta kada kai, idan aka fadi sunan wanda take so, sai tayi shiru, wanda ya nuna shi ta zaba.   KAYAN LEFE Ga al'adar Hausawa, saunayi yan lefe idan aka   yi matsaya akan aure.         Kayan lefe zannuwa ne irin wadanda ake yayi asin da asinda, fatala gwargwadon karfin ango. Ana sa kayan cikin lefen kaba; a kai gidansu amarya. Kafin a kai kayan gidansu amaryar, ana bi da lefen gida-gida ana gani. Saurayin ma zai gayyato abokanansa su gani; ana kiran wane ya fidda lefensa. Haka kuma za a fidda rana guda, wadda za a kai kayan gidan amarya bayan an sanar da su.         Kafin lokacin da za a kai lefen, mata za su taru a gidan iyayen yarinya da marece, inda za su dunguma sukai kayan a gidan iyaye amarya. A bangaren iyayen amarya kuwa, akan fara fada wa wadanda za su tariyar lefen. Idan aka kawo za a bude kayan an gani. Washe-gari kuma 'yanuwa da abokan arziki, za su rika zuwa suna ganin lefen, wanda ya gani zai bada ' yan kudi. Wadannan kayan amarya ne da za ta rika kwaliya da su bayan ta je a gidan ango.   SA LALLE Bisa ga al'adar Hausawa ta aure, duk yarinyar da aka yi wa aure sai ta shiga lalle. Sa budurwa lalle wani babban mataki ne na rayuwar kowace Bahaushiya. Idan yarinya za ta yi auren farin, za a sa ta lalle ko da mutumin da za ta aura, a lokacin yana da aure.         Akan sa yarinya lalle bayan an tabbatar wa saurayi cewa an ba shi yarinya. Lokacin da ya samu tabbatarwa daga iyayenta, zai himmatu wajen kai kayan jin-kira da na lefe. Da zarar saurayi ya kai wadannan kayan za a sa rana wadda za a sa yarinya lalle. Haka kuma akwai wadansu kayan da al'ada ta tanada kamar, buhun lalle, dabino, turare, kwano babba, buhun gero, da wasu kudi suma ana ba dangin saurayi mata su kai gidan su yarinya,   DAUKAN AMARYA Daukar amarya shi ne kai amarya gidan mijinta, bayan ta kammala kwanakin da aka dibar mata cikin lalle.         Lokacin da za a daukar amarya, za a gaya wa 'yan'uwa da abokan arziki, don su hallara daukar amarya. Mata su ke da hidimar daukar amarya, suna tafe suna waka, sai dai wannan waka ta sha bamban da wadda suka zo farko suna yi.   WANKIN ANGO Al'adar Hausawa ce duk saurayi da zai yi aure, dole ne a wanke shi, wankin ango ba karamin abu ba ne ga Hausawa. Kuma kowane saurayi yana shiga lalle, sai dai sau daya a rayuwarsa. Ana wanke saurayi a lokacin da zai yi aure farin. Galibi ana wankin ango da dare bayan daurin aure.   BUDAR KAI Budar kai, shi ne tafiyar da a marya za ta yi gidansu, bayan kwana guda ko biyu, saboda a yi mata gyaran daki da kuma wasu gyare-gyare, irinsu kitso, ko shirye-shiryen zama da mijinta. amarya takan bar gidan mijinta tun da sassafe, wanda wata tsohuwa ce ke zuwa da ta tafi da ita. Akan yi wannan domin bada damar yiwa amarya kitso da kuma wasu gyare-gyare.   GARAR AURE Ita ce garar da aka kai wa miji, domin karfafa dankon soyayya tsakanin miji da mata. Ita wannan walima takan kunshi waina, alkaki, man shanu, man gyada gishiri, dandawa, buhuhuwan shinkafa, gero masara, hadi da wasu kudi.   SAYEN BAKI Ga al'adar Hausawa, idan aka kai amarya gidan mijinta, ba za ta ce uffan ba, sai an saye bakinta. Ana gudanar da sayen baki bayan mata masu sayen baki sun watse, a lokacin ne abokan ango za su kai shi gidansa, a lokacin ne kuma za a saye bakin amarya.   AJO Ajo shi ne taimakon da ake yi wa ango a lokacin da ya yi aure. Kasancewar Hausawa masu kara a tsakaninsu, ya sa kullum idan aka tafi auren abokinsu sukan shiga ajo, domin tallafa wa ango. Akan yi ajo a ranar da ake wankin ango, a wani dandali ko kuma wurin. Lokacin ne 'yan'uwa da abokan arzikin za su taru, domin bada tasu gudumawa, za a rinka yin shela ana cewa “He!” tare da tadin suna

ABUBUWAN DA SUKAFI DAMUN TALAKAWA

gyara sashe

TALAKA SAI HAKURI... Ana yi wa Najeriya  kirari  da uwa mai ba da mama ga dukkan kasashen da ke nahiyar Afirka, kamar yadda Jihar Kano ta yi fice ana yi mata kirari da jalla babbar Hausa, mai mata, mai mota, mai  Dala da Gwauron Dutse ko da me ka zo an fi ka. To a saninmu Najeriya ta yi kaurin suna matuka gaya ,amma ba a nan gizo ke sakar ba, a yau na fahimci tana kasa tana dabo, tana tare da tarin matsaloli iri-iri da suka gallabi ’ya’yanta karancin makamashin hasken wutar lantarki; barazana ga sha’anin ci gaban ilimi; rashin ingantaccen tsaro a kasa; durkushewar kiwon lafiya; rashin aikin yi  ga matasa; rashin gudanar da zaben yadda ya kamata;  faduwar darajar aikin noma. karancin makamashin wutar lantarki a yau a Najeriya kwalliya ta kasa biyan kudin ruwa ballantana na sabulu. Duk da cewa wutar lantarki ita ce linzamin farko na ayyuka da kowane dan Najeriya yake riko da shi, an dogara da komai a kan wutar lantarki. Rashin ta ya haddasa mummunar faduwar  tattalin arzikin ’yan Najeriya, musamman masana’ antu da bangarori iri-iri. Hakan ya yi sanadiyyar tashin  farashin kayan  masarufi a Najeriya, da kuma bude hanya ta shigo da kayayyakin da masana’antun waje suka sarrafa, baje hajarsu a Najeriya da cin karensu babu babbaka, ya kuma sanya kayan da ake sana’antawa  su ki sayuwa. Talakawa sun fada tsaka mai wuya ita ma gwamnati hankalinta ya kasa kwantawa, to wannan da me ya yi kama? Alhali megawat da ake da shi na yunkurin karfin hasken wutar lantarki da muke da shi a da yana da matukar wadatar da Najeriya ciki har tsakura wa jamhuriyar Nijar muke yi. Mutuwar masana’antu ya kara yawan alkaluman marasa aikin yi a Najeriya  ya kara yawa. Haka yasa ala tilas masana’ antu dari da sittin da daya( 161) suka tattara komatsansu ala tilas zuwa kasar Ghana da tauraruwarta take ci gaba da haskawa ta fannoni iri-iri. Wannan ya faru karara muna gani gwamanti ta kasa shawo kan lamarin. A bin takaici ba ya karewa a Najeriya, shugaban kasa Alhaji Umaru Musa ’Yar `aduwa ya yi alwashin yin bincike na ba  -sani –ba- sabo game da ba da kwangilolin wutar lantarki da aka yi rub- da- ciki aka yi. Talakawa da masu kishin kasa sun yi matukar maraba da labarin, amma har yanzu babu amo babu labarin sakamakon kwamitin bincike balle a yi tunanin gurfanar da masu laifi marasa kishin kasa  a gaban kuliya manta sabo. Wannan sai a Najeriya! Shin a haka za mu ci gaba da tafiya da kuma tunkaho da uwa ba da mama ga kasashen Afrika? Abin kunya, wai rakumi ya shanye ruwan kaji. An ce idan kura na maganin zawo ta yi wa kanta. Ya kasance mu talakawan Najeriya akwai hakuri, amma fa ba ma bukatar kura ta kai mu bango.  A wata hira kamar almara da aka yi da ambasada Ibrahim Kazaure a gidan rediyon BBC ya shaida wa ’yan Najeriya cewa ’Yar `aduwa yana wani shiri wai abin burgewa na gyaran hasken wutar lantarki  zuwa watan Disamba na shekarar  dubu biyu da tara( 2009) to ansha ruwa kasa tana tsotsewa, rana ba ta karya, a yadda ’yan Najeriya rayuwa ta yi musu daurin mintin tom-tom akwai wata maganar da za ta sanyaya zuciyarsu kuwa a wannan lokaci idan ba su gani a kasa ba. Gashi dai shekarar 2010 ta shigo sai kaka? 2. Barazana ga tabarbarewar sha’anin ilimi, abin yana ci mana tuwo a kwarya ganin yadda a kasafin kudin kasa na kowace shekara ake ware makudan kudade wajen gudanar da harka ilimi, amma talakawa ba sa gani a kasa. A kullum tambayar su a ina kudaden suke makalewa ba tare da sun kai ga inda aka ce ba? To ku sani an yi walkiya mun gane makiyanmu na hakika da ba sa bukatar ’yan Najeriya talakawa su samu ilimi nagari. Duk da cewa ba a kyauta ake nemansa ba, su kuwa mun sani Turawa ne suka dauki nauyin su gaba daya,amma abin mamaki mu fara duba fannin mataki na farko watau firamare, babu kayan aiki, babu albashi mai tsoka ga su kan su malaman da suke koyarwa an maishe su dabbar kiwo. Abin bakin ciki baya karewa shekarun baya da suka gabata aka fito da wani sabon tsari na baiwa karatun a firamare na bai daya kyauta, duk da sanin asusun majalisar dinkin duniya na ba da makudan kudade wajen ganin an cimma ilmantar da yara, haka ita ma Hukumar da ke son ganin cimma muradun  karni watau MDG  tana iya kokarinta wajen ganin an samu nasara. Ba su sani cewa malamai sai a shafe watanni  biyar ba a biya su alawus na dubu goma kacal ya gagari gwamnati; To da haka ake neman cimma burin? Wannan ba zai yiwu ba, sai an yi gyara sosai.  Haka ita ma sakandare, sai ka tarar babu kayan aiki babu kujeru, matsalar dai kusan guda ce illa dan bambance - bambance da ake samu. Ita kuwa jami’a har yanzu ba ta farfado daga nakasar yajin aiki da ta dawo na watanni kusan biyar, bisa bukatu na malaman jami’o’i da suka zayyana wa gwamnati sai ta biya su bukatun su koma aikin. Shi ma akwai rashin albashi mai tsoka; rashin dakunan karatu, da rashin kayan aiki, da sauran abubuwa da suke ci musu tuwo a kwarya.’ Yan kasa sun fiyawan zargin cewa babu ’ya’ yansu a cikin makarantun sun kaisu kasar waje domin su yi karatu, babu yadda za su yi su damu da makarantun cikin gida ko suna gudana daidai, hakika batun ya sanya tashin jijiyar wuya da tabka muhawara a kafofin yada labarai da jaridun ciki da wajen kasarnan na ganin ilimi ya wadata  da kuma yin gyara a fannin ilimi.  mai karatu abin da na ambata na ciwa ’yan Najeriya tuwo a kwarya matuka. Sai dai rokonmu gwamnati ta yi gyara don ci gaban kasarta. 3. Rashin ingantaccen tsaro. Burin kowace gwamnati ce ta fara sa harkar tsaro a sahu na farko-farko domin bankwana da fargaba da kwararowar abokan gaba, ko da kuwa ta soja ce ko farar fula. Ita dai gwamnati ba ta son a fito fili a ce babu cikekken tsaro a kasa duk da cewa mun sani tana iya kokarinta , amma an ce dambu idan ya yi yawa ba ya jin mai. To mu dubi yadda, ba dare babu rana,  ’yan fashi da makami a cikin kasar nan suke sanadiyyar kisan rayukan talaka da masu kudi; yawaitar ’ yan damfara a fili. Ga kuma yawan cafke makamai kamar wanda aka kama a filin jirgin Malam Aminu Kano, jirgi na makare da kayan yaki. Sannan a baya –bayan nan jami’an shige da fice na kwastan a bakin ruwa sun samu nasarar cafke wata kwantena makare da makamai. Abin tambaya shi ne sai a ce za a yi bincike amma sai ka ji shiru da haka zancen yake susucewa. Haka tasa ake cewa tsaro a Najeiya da sauran aiki, su ma gwamnatin ba’a bar su  ba domin sai a wannan lokacine a ka taba samun masu garkuwa  har sai anbiya musu bukatunsu. Ciki ya hada da cafke jami’ar kasar waje, na baya- bayan nan har da sakataren  gwamnatin Jihar Kaduna. To shin ko wane irin mataki gwamnati za ta dauka, domin ’yan kasa sun fusata da wannan lamari na ganin cewa dole gwamnati ita ce da nauyin magance matsasar duk da cewa hakika ga mai karanta jaridu da sauraron gidajen radiyo da talabijin yana gani ko jin yadda jami’an tsaro suke cafke masu laifi sai dai hukunta su shi ne matsalar.

taya ake gudanarda wankin ango a Hausa

gyara sashe

Taya ake gudanarda wankin ango a Hausa 102.91.5.158 22:57, 20 Nuwamba, 2021 (UTC)Reply

Hausa

gyara sashe

Menene toshi 197.210.53.185 09:49, 22 Nuwamba, 2021 (UTC)Reply