Tasi’u Musa Maigari (An haifeshi ranar 25 ga Aprilu 1966) a Fiwuni dake garin Zangon-Daura, karamar hukumar Zango. Ya yi nasara ha karo biyu na zama wakilin karamar hukumar Zangoa Majalisar Jaha daga shekarar 2015 zuwa yau. A Disamba, 2018, ya samu nasarar zama kakakin majalisar Jihar Katsina na majalisa ta bakwai.[1][2] Ya jagoranci Kwamitin Lafiya kafin zaman shi Kakakin Majalisa na Jihar Katsina a Disamba, 2018.[3]

Farkon Rayuwa gyara sashe

Ya fara karatun sa na firamare a Zango One Primary School daga shekarar 1973 zuwa 1978. Daga nan ya zarce SardaunaMemorial College (SMC) dake garin Kaduna daga shekarar1978 zuwa 1983. Ya kuma halarci Kaduna Polytechnic dagashekarar 1985 zuwa 1988 in da ya anshi shedar kamala National Diploma a fagen Business Administration.

Ayyuka da Mukamai gyara sashe

Dankasuwane kafin shigar shi siyaysa. Ya rike matsayin Darakta a Fuyuni Compani 1988 zuwa yau.

Manazarta gyara sashe