Tasi’u Ibrahim Zabainawa (an haifeshi ranar 1 ga watan Fabrairun shekarar 1964) a Zabainawa da ke ƙaramar Hukumar Minjibir a Jihar Kano.[1]

Karatu gyara sashe

Ya kuma halarci Makarantar Firamare ta Zabainawa Inusa daga shekarar 1974 – 1980 da Kwalejin Malamai ta Garki daga shekarar 1980- 1985. Bayan kuma kammala Jarrabawar Sakandire ta biyu Zainabawa ta shiga takardar shaidar kammala karatu ta ƙasa a tsohuwar Kwalejin Ilimi ta Jihar Kano Kumbotso. [2]

Aiki da Siyasa gyara sashe

Ya kuma yi aiki da ma'aikatar ilimi ta Kano kafin ya wuce Jami'ar Usmanu Ɗanfodiyo da ke Sokoto, inda kuma ya yi digiri a fannin kimiyyar noma.

Bayan rasuwar Honorabul Hamisu Garba Gurjiya a shekarar 2016, wanda ya wakilci karamar hukumar Minjibir a majalisar dokokin jiha. Honorabul Tasi’u zabainawa ya nemi kujerar da ba kowa akai A wani zabe mai cike da cece-kuce a jihar Kano, Honarabul Tasi’u Ibrahim ya lashe kujerar dan majalisar dokokin jihar Kano mai wakiltar karamar hukumar Minjibir a shekarar 2016-2019. [3] sannan kuma yakuma lashe wani zaɓen a shekarar 2019 duka a karkashin jam'iyyar APC.

Manazarta gyara sashe

  1. https://www.shineyoureye.org/person/tasiu-ibrahim-zabainawa
  2. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2021-11-05. Retrieved 2021-11-05.
  3. https://freedomradionig.com/kanoyan-majalisun-dokoki-sun-karbi-rantsuwa