Takarda
Takarda wani siririn abu ne da ake kirkira daga ta hanyar sarrafa sinadarai da makamantansu wanda ake samarwa daga itace, tsumma, ganye, ko sauran nau'in kayan lambu da ake samu a cikin ruwa. Takarda abu ce fara tas da galibi ake rubutu da ita, duk da a wani lokaci akanyi wasu abubuwan da takarda bakasance sai rubutu ba to amman galibin takardu anyi su ne domin rubutu.[1] kuma ana anfani da takarda domin yin zane-zane, da kuma buga rubutu. Sannan kuma takarda yana da bango na kariya saboda kar ya yi datti ko kuma ya yage da sauransu.
Takarda | |
---|---|
material (en) | |
Bayanai | |
Ƙaramin ɓangare na | manufactured product (en) |
Amfani | substrate (en) , insulation (en) , mulch (en) , building material (en) , fasaha, product packaging (en) , Tsafta, banknote (en) , wallpaper (en) , writing surface (en) , painting support (en) da information storage medium (en) |
Suna saboda | papyrus (en) |
Kayan haɗi | wood fiber (en) , flax (en) , dye (en) da bleach (en) |
Karatun ta | paper studies (en) |
Time of discovery or invention (en) | 141 "BCE" |
Fabrication method (en) | papermaking (en) |
Described at URL (en) | vnexpress.net… da sdcvietnam.com… |
Hashtag (en) | Paper da Papier |
Has characteristic (en) | hygroscopy (en) , flammability (en) , compliance (en) da permeability (en) |
Tarihin maudu'i | history of paper (en) |
International Classification for Standards (en) | 85.060 |
Recycling code (en) | 22 |
MCN code (en) | 4707.10.00 |
Duk da cewa a da ana samar da fallen takarda ne kacal da hannu, a yau ana kirkirarsu ne da yawa da manyan ijina, wasu suna kai wa fadin mita 10, suna aiki a mita 2000 a kowanne minti sannan a samar da kuma har ton 600,000 a shekara. Abu ne mai taushi da ke da amfani da dama, wanda ya hada da wallafe-wallafe, zane, jaka, ado, rubutu da goge-goe. Har wayau ana amfani da shi a matsayin fallen tace abu (filter paper) allon bango, fallen takardu, tsumman ban daki, kudi, da dai sauran sarrafe-sarrafe na ma'aikatu da dama.
Tarihi
gyara sasheTarihi mafi tsawo dangane wanda aka sani da burbushin takardu irin na zamanin nan ya samo asali ne a karni na biyu kafin zuwan Yesu a Birnin Sin.