Suleiman Dikko (An Haifeshi ranar 31 ga watan Disamba, 1955), ɗan Najeriya ne wanda shine Babban Alkalin kotun Jihar Nasarawa a yanzu.[1][2]

Suleiman Dikko
Rayuwa
Sana'a
Sana'a mai shari'a

A shekara ta 2019 Dikko ya yi barazanar korar alkalan da sukayi latti wajen zuwa kotu domin sauraren kara. Ya kuma gargadi ƴan sandan Najeriya da cewa zai daina sanya hannu a kan sammacin kama masu laifi da jinkirtawa wajen gurfanar da wadanda ake zargi da laifin da aka riga aka tsare a gidan yari.[3][4]

A watan Fabrairun shekara ta 2019, ƙungiyar ma’aikatan shari’a ta Najeriya (JUSUN) ta yi kira da a kori Dikko daga muƙaminsa na matsayin babban alkali saboda rage albashin ma’aikatan shari’a ba bisa ƙa’ida ba.[5] A cikin wannan watan, an hana Dikko shiga ofishinsa na sa'o'i kafin daga bisani a ba shi damar shiga ofishinsa bayan ya roƙi ma'aikatan shari'a da suka yi zanga-zangar.[6]

A watan Mayun shekara ta 2020, Dikko ya yi afuwa ga fursunoni guda 20 a jihar Nasarawa a wani mataki na rage cunkoso a gidajen yari.[7][8]

Aiki gyara sashe

An kira Dikko zuwa kungiyar Lauyoyin Najeriya ga watan Oktoba shekara ta 1986. An nada shi Alkalin Babbar Kotun Tarayya da ke Lafiya a Jihar Nasarawa a watan Afrilun shekara ta 1986, wanda ya jagoranci Babbar Kotun Tarayya mai lamba 1.[9]

Manazarta gyara sashe

  1. "Justice Sulaiman Dikko Archives". TheCable. Retrieved 2020-06-23.
  2. "Nasarawa Chief Judge discharges 14 inmates". Punch Newspapers. 5 March 2019. Retrieved 2020-06-23.
  3. "Nasarawa CJ threatens to sanction judges over sitting late". The Guardian Nigeria News - Nigeria and World News. 2019-10-07. Retrieved 2020-06-23.
  4. "Nasarawa CJ threatens to sanction judges over sitting late". The Guardian Nigeria News - Nigeria and World News. 2019-10-07. Retrieved 2020-06-23.
  5. "JUSUN demands sack of Nasarawa chief judge". guardian.ng. 8 February 2019. Retrieved 2020-06-23.
  6. "Protesting Workers Lock Nasarawa Chief Judge In His Office". Sahara Reporters. 2019-03-04. Retrieved 2020-06-23.
  7. "Nasarawa Chief Judge pardons 20 inmates | Premium Times Nigeria". 2018-03-08. Retrieved 2020-06-23.
  8. "Nasarawa Chief Judge Frees 16 Inmates". Channels Television. Retrieved 2020-06-23.
  9. "The Judiciary – Official Website of Nasarawa State". Retrieved 2020-06-23.