Suad Abdi
Suad Ibrahim Abdi 'yar gwagwarmayar kare hakkin mata ce daga kasar Somaliya. Ta kasance wakiliyar kasar na kungiyar Progressio kuma mai fafutuka haka zalika mai aiki don buɗe dimokuradiyya ga mata a kasar sama da shekaru 25. Ta yi takara don samun gurbi a majalisa daga Maroodi Jeex a zaben shekarar 2021.
Suad Abdi | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Somaliland, |
ƙasa | Somaliland |
Sana'a | |
Sana'a | ɗan siyasa |
Ayyuka
gyara sasheSuad Ibrahim Abdi ta kasance mai fafutukar kare hakkin bil'adama a Somaliland tun daga shekara ta 1996. Ita memba ce ta Cibiyar Mata ta Kasa ta Somaliland (Nagaad) wacce ta taimaka wajen ganowa a shekarar 1997. [1] Ita ce wakiliyar kasar Somaliland na kungiyar Progressio, wata kungiya mai zaman kanta ta kasa da kasa da ke yakin neman dimokuradiyya a kasar.[1][2] Kungiyatr Progressio ta samar da kwararru don tallafawa aikin kungiyoyin cikin gida da ke aiki a fagen kuma ta samar da masu kallo don Zaben shugaban kasa na Somaliland na 2010 wanda ya ayyana kyauta da adalci.[1]
Abdi na kamfen ko neman yaki don aiwatar da kashi 20% na 'yan majalisa na Somaliland don kasancewa mata. A halin yanzu memba ɗaya ne kawai daga cikin 164 mata. Majalisar Dattawa (gidan sama) ta toshe takardun majalisa guda biyu da suka gabata ko kuma sun ƙare lokacin muhawara. Abdi ta ce za ta tsaya a Zaben 2015 (wanda aka jinkirta zuwa 2017) amma ba za ta nemi zama ministan gwamnati ba.
Manazarta
gyara sashe- ↑ 1.0 1.1 1.2 "Somaliland's secret recipe for stability". Progressio. 3 October 2011. Retrieved 21 November 2017.
- ↑ Cite error: Invalid
<ref>
tag; no text was provided for refs namedguardian