Soyaki
Soyaki Sarkin Kano ne a Masarautar Kano wanda yayi mulki a shekara ta 1652.
Soyaki | |
---|---|
Rayuwa | |
ƙasa | Sarautar Musulunci ta Kano |
Sana'a |
Tarihin Rayuwa a Tarihin Kano
gyara sasheA ƙasa tarihin Soyaki daga Palmar a shekara ta 1908 na fassara turanci akan tarihin kano.[1]
Soyaki shine Sarki na 34 a masarautar Kano, sunan mahaifiyarsa Fatsuma. Kukuna ya gudu zuwa Zukzuk. Soyaki ya yi wata uku yana sarauta sai sarakunan Kano suka haɗu suka yi shawara a kansa. Manyansu kuwa su ne Galadima Wari, kakan Kofakani, Ɗan Iya Babba, Makama Mukhtari da Sarkin Dawaki Gogori. Suka aika mashi da ɗan saƙo a asirce zuwa ga Mohamma Kukuna, wanda nan take ya nufi Gaya. Sarkin Gaya ya tare shi a tattakinsa zuwa Kano. Sai Madawakin Kano ya ji haka, ya tara mutanen Kano, ya ba su labari. Suka ce, "Mun ji." Ya ce, "Me kuke shawara?" Suka ce: "Shin, bãzã mu fita ba a gabãnin su matso birnin." Madawaki ya ce, "Madalla." An gwabza faɗan a Hotoro. Mutanen Kano sun gudu suka bar Madawaki Kuma. Kukuna ya jefe shi da mashi. Sai ya ji tsoron a kashe shi, kuma ya yi ƙoƙarin tserewa. Kukuna ya bi shi. Madawaki yayi wa Kofan Kawayi ihu da jama'a a rufe masa ƙofa, kada Mohamma Kukuna ya shigo. Kukuna kuwa ya shiga kafin a rufe kofar ya isa fada. Ya sami Sarki Soyaki a Giddan Ma-Shikashikai, tare da fādansa.
Manazarta
gyara sashe- ↑ Palmer, Herbert Richmond, ed. (1908), "The Kano Chronicle", Journal of the Royal Anthropological Institute of Great Britain and Ireland, 38, pp. 58–98 – via Internet Archive; in Google Books. This article incorporates text from this source, which is in the public domain.