Souad Bendjaballah
Souad Bendjaballah lauya ce 'yar kasar Aljeriya, mai fafutukar kare hakkokin mata kuma 'yar siyasa.
Souad Bendjaballah | |||||
---|---|---|---|---|---|
| |||||
Rayuwa | |||||
ƙasa | Aljeriya | ||||
Karatu | |||||
Harsuna | Faransanci | ||||
Sana'a | |||||
Sana'a | masana, ɗan siyasa da Mai kare hakkin mata |
Tarihin rayuwa
gyara sasheSouad memba ne na ƙungiyar bincike Tarihin mata a Bahar Rum tare da Fatima-Zohra Guechi kuma ta halarci wannan taron a watan Nuwamba 1999 a Jami'ar Constantine 1.[1] [2] A ranar 8 ga watan Oktoba, 2003, an nada ta Ministar Delegate ga Ministan Ilimi mataki na sama, mai kula da binciken kimiyya . Ta rike wannan matsayi har zuwa shekarar 2012. A ranar 4 ga Satumba, 2012, an naɗa ta Ministar Haɗin kai, Iyali da Matsayin Mata a ƙarƙashin gwamnatin Abdelmalek Sellal. An sake naɗa ta kan mukamin a karkashin gwamnati ta biyu ta Abdelmalek Sellal yayin da aka yi kwaskwarima na Satumba 11, 2013. Ta rike wannan matsayi har zuwa watan Mayun na shekarar 2014.
A shekarar 2017 ta kasance ministar hadin kai.
Manazarta
gyara sashe- ↑ Fatima Zohra Guechi, « Groupe de recherche « Histoire des femmes en Méditerranée », Insaniyat / إنسانيات, 9, vol. 9, 1999, p. 149-151
- ↑ Fatima Zohra Guechi, « Femmes du Maghreb », Clio. Femmes, genre, histoire, vol. 9, 1999