So
So tabbas kalmar So nada wata So,nada wata daraja da baiwa wadda ta dade tana bawa malaman soyayya wahala bayyana ta ga dalili kuwa,shine:- Sabanin ra'ayoyin da ake samu daga bangarori dabam dabam na mallaman soyayya ko kuma ince masana soyayya a takaice. Hakan yasa ma'anar So tazo da bayanai dabam dabam, inda wannan dalilin yasa masu karatun littafan soyayya suka kasa gane ainihin ma'anar So. Koda yake So yazo da ma'anoni dabam dabam. Amma zamu iya cewa ma'anar so itace tsananin kauna da bukatar kusantar wani mutum. So", wata iska ce mai yawo wanda babu wani dan adam ko dabba da bai shake ta ba. Kusan ince so hantsi ne leka gidan kowa.Kuma So tsurone, hakana yayi daidai da fadar wani marubuci inda yace"So yakan tsuro har yayi saiwoyinsa a cikin zuciyar masoya, saboda haka idan aka tunbudo shi, shi ma sai ya tunbuko zuciyar. Saboda haka sai in ba'ayi sa'a ba sai a rasa Rai. Sannan Kuma bai kyale kowa ba, ba babba ba, ba yaro ba, ba mutum ba, ba aljani, ba dabba ba kai har tsuntsaye na soyayya!. So yana da hadari idan ba'a yi shi da hankali ba. Ga wasu kirarin So: 1. Soyayya ruwan Zuma 2. So gubace 3. So yayi Kama da Madara 4. So mai hana ganin laifi 5. So ginshikin rayuwa 6. So Hakimin zuciya 7. So aljannah duniya da dai sauran su.[1]
Soyayya | |
---|---|
advanced emotion (en) da theme (en) | |
Bayanai | |
Ƙaramin ɓangare na | experience (en) , affection (en) da Emotion |
Bangare na | theory of emotion (en) da psychology terminology (en) |
Has characteristic (en) | intimacy (en) |
Hannun riga da | Kiyayya |
Alamomin So kamar haka
gyara sashe- Yawan kallo musamman a sace
- Yawan Ambato
- Faduwar gaba yayi da aka ambata masoyi, kuwa sunan shi.
- Yawan tunanin abunda aka kamu da sonshi.
- Tausayin: idan kaga mutum Yana yawan tausayin ka to yana sonka
- Kunya: idan kaga kunya ta shiga tsakani masoya biyu to akwai soyayya ta gaskiya
Abubuwa dake gyara soyayya
gyara sasheAbubuwa dake bata soyayya
gyara sashe1. Karya 2. Yaudara 3. Rashin tsafta. 4. Rashin yarda da Kuma zargi dadai sauran su.
Hotuna
gyara sashe-
Wasu Masoya a filin jirgin Sama
-
Wasu Masoya
Manazarta
gyara sashe- ↑ Jessica, Murphy (19 February 2020). "An gano maganin ciwon so". bbc hausa. Retrieved 23 July 2021.