Shevchenko National Preservation

Shevchenko National Preserve (ukr. Шевченківський національний заповідник; Shevchenkivskyi natsionlnyi zapovidnyk) wani wurin shakatawa ne na kasa dake kusa da Kaniv (Ukraniya), ta shahara a dalilin kabarin shahararren mawaƙin Ukraine Taras Shevchenko da gidan kayan gargajiya da aka sadaukar don tunawa da shi. Jimillar girman wurin ya kai kadada 45, kayan da ake ajiya su. hada da wuraren tarihi guda takwas, kuma tana iyaka da Kaniv Nature Reserve.[1]

Shevchenko National Preservation
Q97496461 Fassara
Bayanai
Farawa 1925
Ƙasa Ukraniya
Wuri
Map
 49°43′59″N 31°30′53″E / 49.733055°N 31.514723°E / 49.733055; 31.514723
Historical country (en) FassaraKievan Rus' (en) Fassara
Historical country (en) FassaraPrincipality of Kyiv (en) Fassara
City of regional significance of Ukraine (en) FassaraKaniv (en) Fassara

Bayanai gyara sashe

A ranar 22 ga watan Mayu, 1861, an binne shahararren mawakin Ukraine Taras Shevchenko a kan tudun Chernecha, wanda daga baya akafi sani da Tarasova. A shekara ta 1884, an gina gidan kayan tarihi na farko na Taras Shevchenko a kan tsaunin Tarasova kuma an gina wani babban abin tunawa na simintin ƙetare tare da Viktor Sichugov. A ranar 10 ga Yuni, 1918, Majalisar Ministoci na Jihar Ukrainian ta amince da kabarin Taras Shevchenko a matsayin dukiyar ƙasa. A watan Agusta 1925 an mayar da Tsaunin Tarasova matsayin wurin shakatawa.[2] [1]

A zamanin yau gyara sashe

Wurin da aka kabe ya kunshi farfajiya a karkashin kulawar Ma'aikatar Al'adu da Bude Idanu ta Ukraine. Sashin State Service for National Cultral Heritage ke kula da sashen.

Wurin shakatawan ya kadance cibiyar al'adu da kuma ilimi, wurin bincike da kuma yawon shakatawa wanda ke bunkasa nazarin tarihin kayan gargajiya na asali na mutanen Ukraine, irinsu ayyukan Taras Shevchenko, da tarihin Tsaunin Chernecha, sannan kuma da kare al'adu sa wuraren tarihi tun daga zamunan baya har zuwa yanzu, da kuma wurare na zahiri wanda suka .[ana buƙatar hujja] haɗa da ayyukan mai zane Hanna Veres.

Kowace shekara gidajen tarihi na Shevchenko National Preserve suna karbar baki fiye da mutum100 dubu masu yawon bude ido daga tsakanin Ukraine da kuma kasashen waje.

Manyan daraktocin Shevchenko National Preserve su hada da:

  • 1989–2005 - Ihor Likhovy[3]
  • 2005–2010 - Maryan Pinyak[4]
  • 2010–2011 - Ihor Renkas[5]
  • 2011-2013 - Vasyl Kolomiets[6]
  • 2014-2015 - Vasyl Tulin[7]
  • 2015–2020 - Maryan Pinyak[4]
  • Tun 2020 - Valentyna Kovalenko[8]

Hotuna gyara sashe

Kara karantawa gyara sashe

Manazarta gyara sashe

  1. 1.0 1.1 SA Bryzhytska. Shevchenkivsky National Reserve in Kaniv. Encyclopedia of the History of Ukraine : in 10 vol. Кyiv : Naukova dumka, 2013. Vol. 10. p. 617. 784 pp. ISBN 978-966-00-1359-9
  2. "Decree of the President of Ukraine "On National Cultural Institutions"". Ukrainian Parliament. October 11, 1994.
  3. Ліховий Ігор Дмитрович" (in Ukrainian). Institute of history of Ukraine.
  4. 4.0 4.1 The director of the Shevchenkivsky National Reserve in Kaniv, Maryan Pinyak, passed away" (in Ukrainian).
  5. "Ihor Renkas has been appointed as a director of the Shevchenko reserve". kaniv.net (in Ukrainian).
  6. "Vasyl Kolomiets has been appointed as a director of the Shevchenko reserve". kaniv.net (in Ukraine)
  7. "New director of Shevchenko Musem in Kaniv is appointed". istpravda.com.ua (in Ukraine)
  8. "Shevchenko National Reserve in Kaniv was headed by Valentyna Kovalenko". procherk.info (in Ukraine).

Hanyoyin haɗi gyara sashe

49°43′53″N 31°30′56″E / 49.73139°N 31.51556°E / 49.73139; 31.51556