Serge Bengono (an haife shi ranar 3 ga watan Agusta, 1977) ɗan wasan tseren Kamaru ne wanda ya ƙware a tseren mita 100.

Serge Bengono
Rayuwa
Haihuwa 3 ga Augusta, 1977 (47 shekaru)
ƙasa Kameru
Sana'a
Sana'a Dan wasan tsalle-tsalle
Athletics
Records
Specialty Criterion Data M
Personal marks
Specialty Place Data M
 

Sana'a/Aiki

gyara sashe

Ya yi takara a gasar Olympics ta bazara ta shekarar 2000 da kuma gasar cin kofin duniya a shekarun 2001 da 2003 ba tare da ya kai wasan karshe ba.[1]

Mafi kyawun lokacinsa shine daƙiƙa 10.25 a tseren mita 100, wanda ya samu a Gasar Wasannin Afirka ta shekarar 1999 a Johannesburg; da dakika 20.89 a cikin tseren mita 200, da aka samu a watan Afrilun 2002 a Knoxville. Shi ma mai riko ne na kasa a tseren mita 4x100, da aka samu a Gasar Cin Kofin Duniya na 1999.[2] A relay ya kuma taka leda a gasar cin kofin duniya ta 1997.

A halin yanzu Serge Bengono mataimakin kocin tsere ne a Jami'ar Jihar Norfolk.[3]

Manazarta

gyara sashe
  1. Cameroonian athletics records Archived 26 September 2007 at the Wayback Machine
  2. Serge Bengono at World Athletics
  3. Evans, Hilary; Gjerde, Arild; Heijmans, Jeroen; Mallon, Bill ; et al. "Serge Bengono Olympic Results" . Olympics at Sports-Reference.com . Sports Reference LLC. Archived from the original on 18 April 2020. Retrieved 10 September 2017.