Senorita(wakar Shawn Mendes da Camila Cabello)
"Señorita" waƙa ce ta mawaƙin kasar Kanada Shawn Mendes da mawaƙiya kuma marubuciyar waka yar kasar Amurka Camila Cabello. An sake ta a ranar 21 ga Yuni, 2019, ta hanyar Island and Epic Records a matsayin na biyu guda(single) daga bugu na deluxe na kundin studio mai taken kansa na uku na Mendes, da jagora guda(single) daga kundin studio na biyu na Cabello Romance (2019) Mendes, Cabello, Charli XCX, Ali Tamposi, Jack Patterson, da masu samarwa Andrew Watt, Benny Blanco, da Cashmere Cat ne suka rubuta.[1]waƙar ta nuna alamar haɗin gwiwar Mendes da Cabello na biyu, bayan "I know what you did last summer" daga kundi na farko na Mendes, Handwritten (2015). "Señorita" ya kai lamba daya a kan Billboard Hot 100 na Amurka, da kuma kan gaba a cikin jadawalin tarihin da ya kafa kasashe 40 a duniya. Tabbataccen multiplatinum ne cikin ƙasashe goma sha uku, gami da Diamond a Australia, Kanada, Faransa, da Mexico, da lu'u-lu'u biyu a Poland. "Señorita" ya sami kyakkyawan bita daga masu sukar kiɗa.wakar ta lashe lambar yabo ta kiɗan Amurka, lambar yabo ta MTV Video Music Awards, lambar yabo ta Zaɓin Jama'a, kuma ta karɓi zaɓi don Kyautar Grammy don Mafi kyawun Ayyukan Pop Duo/Group. Waƙar ita ce babbar waƙa ta 2019 a Malaysia kuma bisa ga Ƙungiyar Ƙasa ta Duniya ta Masana'antar Watsa Labarai (IFPI), ita ce ta uku mafi kyawun siyarwa na 2019 a duk duniya, tare da haɗin tallace-tallace da magudanan waka daidai da raka'a miliyan 16.1 a duniya.[2]Tun daga watan Yuni 2024, ita ce waƙa ta 18 mafi yawan yawo akan Spotify.[3]
Señorita | |
---|---|
single (en) | |
Bayanai | |
Bangare na | Romance |
Laƙabi | Señorita |
Mabiyi | If I Can't Have You (en) da Find U Again (en) |
Ta biyo baya | South of the Border (en) |
Nau'in | pop music (en) |
Mai yin wasan kwaikwayo | Shawn Mendes (en) da Camila Cabello (en) |
Lakabin rikodin | Island Records |
Harshen aiki ko suna | Turanci |
Ranar wallafa | 21 ga Yuni, 2019 |
Furodusa | Benny Blanco |
Charted in (en) | Billboard Hot 100 (en) |
Distribution format (en) | vinyl record (en) , music streaming (en) da music download (en) |
Manazarta
gyara sashe- ↑ "Señorita / Shawn Mendes". Tidal. 21 June 2019. Archived from the original on June 21, 2019. Retrieved June 23, 2019.
- ↑ "IFPI Names Billie Eilish's 'Bad Guy' the "Biggest Global Single of 2019"". Billboard. 2020-03-10. Retrieved 2020-03-10.
- ↑ "List of most-streamed songs on Spotify", Wikipedia, 2021-10-21, archived from the original on 2023-09-08, retrieved 2021-10-21