Selma Harrington
Selma Harrington née Arnautović ita yar ƙasar Bosniya ce kuma mai ƙira. Tana da digiri na uku na PhD Architecture daga Jami'ar Strathclyde da MPhil European Studies daga Kwalejin Trinity Dublin. Ita memba ce ta Hukumar Zartaswa kuma MataimakiyarShugaban Kasa (shekara 2020-21) kuma ta yi aiki a matsayin Shugabar Majalisar Gine-gine ta Turai (ACE) (2010 – 11 da 2012 – 13).
Selma Harrington | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Sarajevo, 16 ga Janairu, 1955 (69 shekaru) |
ƙasa |
Ireland Herzegovina |
Karatu | |
Makaranta | University of Sarajevo (en) |
Sana'a | |
Sana'a | Masanin gine-gine da zane da designer (en) |
Employers | Griffith College Dublin (en) (2009 - ga Yuni, 2017) |
Tarihin Rayuwa
gyara sasheHarrington an haife ta kuma ta girma a Sarajevo. Ta kammala karatun gine-gine shekara (1978) kuma ta sami digiri na biyu shekara (1985) a Jami'ar Sarajevo
Bayan ta yi aikin gine-gine, kayan daki da mai tsara kayayyaki a cikin Sarajevo, ta ƙaura zuwa Harare, Zimbabwe shekara (1991), inda ta kafa nata kamfani mai ƙira wadda ta ƙware a cikin gine-gine, ƙira da gyare-gyare (shekara 1993-99). A cikin shekarun da suka gabata, ta kammala ayyuka a Turai, Afirka da Asiya a fannonin da suka shafi otal da ofisoshi, ƙirar gidaje da kayan daki. Bayan ƙaura zuwa Dublin, Ireland, ta ɓullo da babban fayil na kiyayewa, gyare-gyare da ayyukan ƙira. Hakazalika, ta haɓaka aikin ilimi ta hanyar jagorantar shirin Jagora a fannin gine-ginen cikin gida da kuma yin bincike. Ita memba ce ta Cibiyar Sarauta ta a Ireland (RIAI) kuma Shugabar Wakilin Irish zuwa Majalisar Architects na Turai (ACE).
Selma ta yi aiki a matsayin sakatare-janar na Majalisar Tarayyar Turai Architects (2004-08), Shugabar Cibiyar Zane-zane a Ireland (IDI) - 2003 da kuma Babban Ma'aji na Cibiyar Zane da Nakasa a Ireland (IDDI) a cikin shekaea 2001. [1]
Hanyoyin haɗi na waje
gyara sashe- "Hukumar zartarwa: ACE." An shiga Oktoba 19, shekara 2021. https://www.ace-cae.eu/about-us/executiveboard/ .
- Jami'ar Kasa da Kasa ta Sarajevo. "Selma Harrington daga Kwalejin Griffith Dublin ta ziyarci IUS," Oktoba 22, shekara 2015. https://news.ius.edu.ba/news/selma-harrington-griffith-college-dublin-visited-ius .
- Harrington, Selma. "Yin Ƙari Tare da Karancin Ilimin Gine-gine A Lokacin Kalubale," 65,111,119. Cibiyar Gine-ginen Rum, Chania, shekara 2011.
- https://www.ace-cae.eu/about-us/executive-board/
- https://orcid.org/0000-0002-2936-6482
- https://ulupubih.com/enterijer-dizajn/
- https://ecia.net/about-ecia/identity
Magana
gyara sashe- ↑ "Arnautović-Harrington, Selma (1955)", Ulupubih. (in Croatian) Retrieved 10 March 2012.