Sekou Oumar Sylla (an haife shi 9 ga watan Janairun 1999), ƙwararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne wanda ke taka leda a matsayin mai buga baya na hagu don ƙungiyar Eredivisie SC Cambuur. An haife shi a Netherlands, yana taka leda a tawagar ƙasar Guinea.

Sekou Sylla
Rayuwa
Haihuwa Schiedam (en) Fassara, 9 ga Janairu, 1999 (25 shekaru)
ƙasa Kingdom of the Netherlands (en) Fassara
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
 
Sekou Sylla acikin filin wasa
hutun Sekou Sylla

An haife shi a Schiedam, Sylla ya fara aikinsa a Excelsior Maassluis kafin ya shiga ƙungiyar Eerste Divisie TOP Oss akan kwangilar mai son a lokacin ranin shekarar 2021. [1][2] Ya canza sheka ta kyauta zuwa kulob din Eredivisie SC Cambuur a watan Janairun 2022, inda ya rattaba hannu kan kwantiragin watanni 18. [2][2][3]

Ayyukan kasa da kasa

gyara sashe

An haife shi a Netherlands, Sylla ɗan asalin Guinea ce. Ya yi karo da tawagar kasar Guinea a wasan sada zumunci da suka yi da Afirka ta Kudu a ranar 25 ga watan Maris ɗin 2022.[4]

Manazarta

gyara sashe
  1. "Excelsior Maassluis raakt Sekou Sylla kwijt aan profvoetbal". Voetbal Rotterdam (in Holanci). 20 June 2021. Retrieved 22 January 2022.
  2. 2.0 2.1 2.2 Boeringa, Reon (7 January 2022). "Van amateurs naar Eredivisie: razendsnelle promotie voor Cambuur-aanwinst". Voetbal International (in Holanci). Retrieved 22 January 2022.
  3. van der Doelen, Jaap (7 January 2022). "Amateur Sekou Sylla van TOP Oss naar de eredivisie". Retrieved 22 January 2022.
  4. "Starting Lineups - S. Africa vs Guinea - 25.03.2022". Sky Sports. 2022-03-25. Retrieved 2022-03-26.

Hanyoyin haɗi na waje

gyara sashe