Sale Ahmad Marke (26 ga Janairu, 1963) a ƙauyen Dambaje na ƙaramar hukumar Dawakin Tofa. Ya fito daga unguwar Marke. [1]

Sale Ahmad Marke
Rayuwa
Haihuwa Dawakin Tofa, 26 ga Janairu, 1963 (61 shekaru)
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
littafi akan sale ahmad marke
Sale Ahmad Marke

Karatu da Siyasa

gyara sashe

Ya halarci Makarantar Firamare ta Marke (1970 – 1977) da Makarantar Sakandare ta Garko, 1977 – 1982. Honorabul Marke ya taɓa zama Malamin Makarantar Firamare, Malamin Kiwon Lafiyar Ƙaramar Hukumar kafin shiga siyasa. Daga shekarun 1999 – 2003, an zaɓe shi kansila. [2]

An fara zaɓen Honourable Marke a matsayin ɗan majalissar jiha a shekarar 2007 – 2011. An sake zaɓen shi a 2011 – 2015 da 2015 – 2019 bi da bi. kuma yanzu haka shine Shugaban Kwamitin Aikin Hajji Na jahar kano.

Manazarta

gyara sashe