Sahi Muslim ( Larabci : صحيح مسلم) ɗayan Kutub al-Sittah ne (manyan hadisai shida masu tarin yawa) a cikin Musulman Sunni .[1] Yana da mahimmancin gaske tsakanin musulmin Sunni kuma ana ɗaukar sahihan hadisi mafiya inganci bayan Sahi al-Bukhari . Muslim bn al-Hajjaj ne ya tattara su (815-875), wanda aka fi sani da Imam Muslim . Sahih Muslim, tare da Sahih al-Bukhari ana kiransa Sahihayn.[2][3][4]

Sahi Muslim
Murfin Sahi Muslim

Imamu Muslim ya tara hadisi kusan 300,000. Daga cikin waɗannan, an haɗa 4000 a cikin tarin. A cewar Munthiri, akwai adadin hadisai 2,200 (ba tare da maimaitawa) a cikin Sahih Muslim ba. A cewar Muhammad Amin, akwai ingantattun hadisai 1,400 waɗanda aka ruwaito su a cikin wasu litattafai, galibi manyan hadisan guda shida.[5]

Manazarta

gyara sashe
  1. A.C. Brown, Jonathan (2014). Misquoting Muhammad: The Challenge and Choices of Interpreting the Prophet's Legacy. Oneworld Publications. p. 257. 08033994793.ABA. [...] the Sahihayn, the two authentic Hadith compilations of Bukhari and Muslim bin Hajjaj that Sunni Islam has long declared the most reliable books after the Qur'an.
  2. A.C. Brown, Jonathan (2014). Misquoting Muhammad: The Challenge and Choices of Interpreting the Prophet's Legacy. Oneworld Publications. p. 257. 08033994793.ABA. [...] the Sahihayn, the two authentic Hadith compilations of Bukhari and Muslim bin Hajjaj that Sunni Islam has long declared the most reliable books after the Qur'an.
  3. Ahmad, K. J. (1987). Hundred Great Muslims. Des Plaines, Ill.: Library of Islam. 08033994793.ABA.
  4. Abdul Mawjood, Salahuddin `Ali (2007). The Biography of Imam Muslim bin al-Hajjaj. translated by Abu Bakr Ibn Nasir. Riyadh: Darussalam. 08033994793.ABA.
  5. "عدد الحديث الصحيح - إحصائيات متنوعة". www.ibnamin.com.