Fayil:Ciyawar Sabe.jpg
Ciyawar Sabe

Saɓe wata ciyawa ce mai albarka da kwarjini. A cikin fadama take fitowa wajen da babu noma ta kan yi baƙi ta yi kyau sosai amma ba ta daukan lokaci mai tsaho sai ta yi ja, kenan ta fi son wajen da aka yi noma, idan ta fito ta wajen da noma yake za ka ga ciyawan saɓe baƙiƙirin  tsanwa shar gwanin sha'awa, ganyenta tana da laushi da daɗin taɓi domin bata da ƙaya bata da kaifi.

Taken bushe a lokacin rani idan iskan yamma ya buga takan yi ƙonshi ta fitar da kai kaman sauran ciyayi 'yan uwanta, haka ma takan yi ƙwaya ƙanana kanana, ƙwayan yakan zube a nan inda ya fito kuma su ne suken zam irin da zai sake fitowa damuna mai zuwa idan Allah ya kai mu.

Shawara ga malaman gona da su kula ga ma su yin feshi ga irin waɗannan ciyayin a lokacin da ba su riga sun zubar da ƙwayoyinsu ba, tabbas wata rana duniya za ta nemi ire-iren waɗannan ciyayin a rasa.[1]

  1. https://www.amsoshi.com/2023/09/sabe.html?m=1