ruwan sama ruwa ne da ke sauka daga sama wanda Allah (S.W.T) shi ne ya ke saukar da shi a kowane lokaci dare ko rana, wani lokaci ya yi yawa wani lokaci kuma ya yi kadan, amma mafi yawa ya fi zuwa da hadari, wanda hausawa suke mashi lakabi da (ruwa kaman da bakin kwarya). Sai kuma yayyafi, shi yayyafi mafi akasari yana zuwa ne a hadarin da bai saukar da ruwa ba, sai kuma misali lokacin marka-marka shi kuma a wannan lokacin zaka ga ruwa ba dare ba rana. A wani lokaci ruwan yayi karfi wani lokacin kuma baya yin karfi, to wanda bai yi karfin ba shi ne ake kira da yayyafi.[1][2]

Wikidata.svgruwan sama
natural phenomenon (en) Fassara
08152 Bukowsko (powiat sanocki).jpg
Bayanai
Ƙaramin ɓangare na precipitation (en) Fassara
Yana haddasa ambaliya da rainwater (en) Fassara
Amfani hydroelectricity (en) Fassara, Noma, water supply (en) Fassara, Ginawa da laundering (en) Fassara
Rukunin da yake danganta rukuni:Waƙoƙi game da ruwan sama
Facet of (en) Fassara yanayi
ruwan sama na zubowa a kan titi
yara suna wasa a ruwan sama

.

A Larabci ana kiransa da "مطر".

HadariGyara

Shi dai hadari shi ne kusan ace ginshikin ruwan sama wanda mafi yawan ruwan saman da ake yi sai hadari ya hadu ya taso yayi iska sannan sai ruwa ya zo, wani lokaci a hade da iska wani lokacin kuma zallan ruwan ne. Menene Hadari ? Hadari dai shi ne haduwar giza-gizai waje daya musamman bakaken giza-gizai sai su dunkule waje daya su tado da iska daga nan bayan iska sai ruwa ya biyo baya, sai dai akwai abunda ke kawowa hadari cikas shi ne bakan gizo wanda zaka ganshi wani ja-ja da yalo-yalo kala dai kusan uku, to idan ya kewaye hadari zaka ga sai dai hadarin nan yayi yayyafi, to wannan yayyafin hausawa na kiran shi "aman bakan gizo".

Marka-MarkaGyara

Wani dan tsakaitaccen lokaci ne na damina inda ake yin ruwa akai-akai ba tsakaitawa.

ManazartaGyara

  1. https://www.dw.com/ha/ambaliyar-ruwan-sama-ta-kashe-mutane-12-a-najeriya/a-50263746
  2. "Hukumar kula da yanayi tayi hasashe". BBC Hausa. Retrieved 20 March 2021.

.