Rimac Nevera
Rimac Nevera (lafazi: [rǐːmat͡s něʋeːra] ) motar wasa ce mai amfani da wutar lantarki kamfanin kere keren motoci na Croatian Rimac Automobili shine ya qera wannan mota . An fito samfurin farko na motar a watan Agusta 2021. Ba a tsaida samarwar motar ba sadda suka kai kimanin kala 150. Bayan kammala gwajin hadari don homologation, Rimac ya shirya kawo wa abokan ciniki Nevera a shekarar 2022. An kawo kirar farko na Nevera a cikin Agusta 2022. An fara kaiwa zuwa Amurka a watan Yuni 2023. An kera Nevera a cikin masana'anta guda daya kuma ana samar da kira daya duk mako kamar yadda Pininfarina Battista, wanda itama anyi ta akan tsari daya ne.
Rimac Nevera | |
---|---|
automobile model (en) | |
Bayanai | |
Ƙaramin ɓangare na | mota, electric car (en) da battery electric vehicle (en) |
Ƙasa da aka fara | Kroatiya |
Manufacturer (en) | Rimac Automobili (en) |
Brand (en) | Rimac Automobili (en) |
Location of creation (en) | Sveta Nedelja (en) |
Powered by (en) | electric motor (en) |
Shafin yanar gizo | rimac-automobili.com… |
Source of energy (en) | Batirin lantarki |
Dubawa
gyara sashe-
Rimac C II
An bayyana motar a 2018 Geneva Motor Show a matsayin Rimac C_Two; Daga baya aka sake mata suna zuwa Nevera bayan kaddamar da shi. Mota ce ta biyu bayan Rimac Concept One . Rimac ya bayyana ci gabansa a matsayin "neman matukar kwarewar tukin motar lantarki".