Reo Addai Basoah

Dan siyasan Ghana

Reo Addai Basoah (1936 - Yuli 30, 2002) dan majalisa ne mai wakiltar mazabar Kumawu na yankin Ashanti na Ghana.[1] Ya kasance memba na majalisa ta biyu da ta uku na jamhuriya ta 4 ta ƙasar Ghana.[2][3] Ya kuma kasance shugaban kwamitin kudi na majalisar dokokin Ghana a shekarar 1997 har zuwa lokacin da ya zama dan majalisa bayan ya lashe zaɓen shekarata 1996.

Reo Addai Basoah
Member of the 3rd Parliament of the 4th Republic of Ghana (en) Fassara

7 ga Janairu, 2001 - 31 ga Augusta, 2002
District: Kumawu Constituency (en) Fassara
Election: 2000 Ghanaian general election (en) Fassara
Member of the 2nd Parliament of the 4th Republic of Ghana (en) Fassara

7 ga Janairu, 1997 - 6 ga Janairu, 2001
District: Kumawu Constituency (en) Fassara
Election: 1996 Ghanaian general election (en) Fassara
Rayuwa
Haihuwa 1934
Mutuwa 30 ga Yuli, 2002
Karatu
Makaranta University of Cambridge (en) Fassara 1961) unknown (en) Fassara : ikonomi
Yale University (en) Fassara 1962) unknown (en) Fassara : ikonomi
King's College London (en) Fassara master's degree (en) Fassara : ikonomi
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa da Mai tattala arziki
Imani
Jam'iyar siyasa New Patriotic Party

[1][2][3][4]

Basoah ya rasu a asibitin koyarwa na Korle-Bu a ranar 30 ga Yulin, shekarar 2002 bayan gajeriyar rashin lafiya.[5]

Rayuwar farko da ilimi

gyara sashe

An haifi Basoah a shekara ta 1936 kuma ya yi karatu a Kwalejin Fasaha ta Cambridge da ke birnin Landan. Ya kuma yi karatu a Jami'ar Yale kafin ya wuce Kwalejin King da ke Cambridge don yin kwas a fannin Tattalin Arziki. A shekarar 1962 ya zama Barrister-at-Law a Lincoln's Inn. Basoah ya kuma yi aiki a matsayin masanin tattalin arziki a kwamitin tattalin arzikin Commonwealth da ke birnin Landan da kuma bankin duniya a Washington, D.C. daga shekarar 1965 zuwa 1972.[6]

Aikinsa na siyasa ya fara ne a shekarar 1992 lokacin da ya fara shiga majalisar a matsayin kwamishinan hukumar kasuwanci ta jiha.[7] Daga baya aka nada shi shugaban kwamitin kudi a shekarar 1997.[8] Ya kuma tsaya takara a zaben shekarata 1996 a matsayin wakilin mazabar Kumawu a kan tikitin sabuwar jam’iyyar Patriotic Party kuma ya samu kuri’u 15,025 na kuri’un da aka kada a waccan shekarar. Daga nan sai ya sake tsayawa takara a zaben shekara ta 2000 ya ci gaba da rike kujerarsa a karo na biyu da kuri’u 13,554 wanda ya samu kashi 57.80% na kuri’un da aka kada. Ya rasu ne kafin karshen wa’adinsa na majalisa.[9][10]

Basoah ya rasu ne a Asibitin Koyarwa na Korle-Bu bayan an kwantar da shi na tsawon kwanaki uku sakamakon gajeriyar rashin lafiya.[11][12]

Manazarta

gyara sashe
  1. "King's College, Cambridge Annual Report 2017" (PDF).
  2. "Kumawu Besoro to get community centre" (in Turanci). Retrieved 2020-09-01.
  3. "Government's policy on works and housing lacks focus - Bartels". www.mclglobal.com. Retrieved 2020-09-01.
  4. "MP for Kumawu is Dead". www.ghanaweb.com (in Turanci). 2002-08-01. Retrieved 2020-09-01.
  5. "Kumawu MP laid to rest". www.ghanaweb.com (in Turanci). 2002-09-08. Retrieved 2020-09-03.
  6. "King's College, Cambridge Annual Report 2017" (PDF).
  7. "King's College, Cambridge Annual Report 2017" (PDF).
  8. "MP for Kumawu is Dead". www.ghanaweb.com (in Turanci). 2002-08-01. Retrieved 2020-09-01.
  9. FM, Peace. "Parliament - Kumawu Constituency Election 2000 Results". Ghana Elections - Peace FM. Retrieved 2020-09-01.
  10. "Ghana Election kumawu Constituency Results". www.graphic.com.gh. Retrieved 2020-09-01.
  11. "MP for Kumawu is Dead". www.ghanaweb.com (in Turanci). 2002-08-01. Retrieved 2020-09-01.
  12. "Kumawu Besoro to get community centre" (in Turanci). Retrieved 2020-09-01.