Phocas Nikwigize
Phocas Nikwigize (23 ga watan Agusta 1919 - 30 Nuwamba 1996) bishop ne a Cocin Roman Katolika, kuma ɗan kasar Ruwanda ne.
Phocas Nikwigize | |||
---|---|---|---|
5 Satumba 1968 - 5 ga Janairu, 1996 ← Joseph Sibomana (en) - Kizito Bahujimihigo (en) → Dioceses: Roman Catholic Diocese of Ruhengeri (en) | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Masarautar Ruwanda, 23 ga Augusta, 1919 | ||
ƙasa | Ruwanda | ||
Mutuwa | Goma (birni), 30 Nuwamba, 1996 | ||
Sana'a | |||
Sana'a | Catholic priest (en) da Catholic bishop (en) | ||
Imani | |||
Addini | Cocin katolika |
Nikwigize an haife shi a Muhango, Rwanda, kuma an naɗa shi firist a ranar 25 ga watan Yuli 1948. An nada shi bishop na Diocese na Ruhengeri hakazalika an nada shi bishop a ranar 30 ga Nuwamba 1968. Nikiwigize ya ci gaba da kasancewa a wannan mukamin har sai da ya yi ritaya a ranar 5 ga watan Janairun 1996.
A ranar 27 ga watan Nuwamba 1996, ya tafi don sake shiga kasar Ruwanda tare da masu wa’azi a mishan lokacin da wasu sojojin Kishin Ruwanda suka kama shi kuma aka yi imanin an kashe shi a ranar 30 ga watan Nuwamba 1996.[1][2]