Philip IV na Sipaniya
Philip IV ( Spaniyanci, Yaren portugal Filipe; Afrilu 8, 1605 – 17 Satumba 1665), wanda kuma ake kira Planet King (Spanish: Rey Planeta ), shi ne Sarkin Spaniya daga shekarar alif 1621 zuwa mutuwarsa da (a matsayin Philip III ) Sarkin Portugal daga 1621 zuwa 1640. Ana tunawa da Philip saboda goyon bayan da ya bada ga fasaha, ciki har da masu zane irin su Diego Velázquez, da mulkinsa na Spaniya a lokacin Yaƙi na tsawon Shekaru Talatin . A lokacin mutuwarsa, Daular Spain ta kai girman kusan murabba'in kilomita miliyan 12.2 (4.7 mil miliyan murabba'in mil) a fadin kasa amma a wasu bangarorin yana raguwa, tsarin da Philip da kanshi ya ba da gudummawa ta hanyar gazawarsa wajem samun nasarar sake fasalin cikin gida da na soja.
Rayuwarsa
gyara sasheAn haifi Philip IV a fadar masarautar Valladolid, kuma shi ne ɗa na farko ga Philip III da matarsa, Margaret na Ostiriya . A cikin shekarar alif 1615, lokacin yana ɗan shekara 10, Philip ya auri Elisabeth ’yar Faransa ’mai shekaru 13. Kodayake dangantakar ba ta kasance kusa ba, wasu sun nuna cewa Olivares, babban ministansa, daga baya ya yi ƙoƙari ya raba su don ya cigaba da mulkinsa, yana ƙarfafawa cewa Philip ya dauki kwarkwarori a maimakon mata, wanda yana da kusan 'ya'ya 30. [1] Filib yana da 'ya'ya goma da Elisabeth, wanda kwara ɗaya ne namiji, Balthasar Charles, wanda ya mutu yana da shekaru goma sha shida a 1646. Mutuwar ɗansa ta girgiza sarkin sosai, wanda da alama uba ne nagari. Elisabeth ta shirya makirci da wasu manyan Mutanen Espanya don cire Olivares daga kotu a 1643, kuma na ɗan gajeren lokaci ta yi tasiri sosai a kan Filib; A lokacin mutuwarta kuwa, duk da haka, ta rasa kimar ta, bayan wani yinkuri da magajin Olivares da ɗan'uwansa Luis de Haro suka yi. [1]