Peggy Phango (28 Disamba 1928 - 7 Agusta 1998) ƴar wasan kwaikwayo ce kuma mawaƙiya ta Afirka ta Kudu, wacce daga shekarar 1960 ta kasance a Ingila.

Rayuwar farko gyara sashe

An haifi Peggy Phango a Orlando, Transvaal, Afirka ta Kudu. Ta sami horo a matsayin ma'aikaciyar jinya, amma kuma ta rera waƙa a kulab ɗin jazz, a matsayin budurwa. [1] [2]

Rayuwa ta sirri gyara sashe

Peggy Phango ta auri jazz pianist Johnny Parkera shekarar 1965, a matsayin matarsa ta biyu. Suna da ƴaƴan mata biyu, Abigail da Beverly. Phango ta Mutu a shekarar 1998 a London, tana da shekaru 69 a duniya.[3]

=Manazarta gyara sashe

  1. Tom Vallance, "Obituary: Peggy Phango" The Independent (2 September 1998).
  2. Michael Knipe, "From Tradesman's Daughter to Stage Queen" Mail & Guardian (21 August 1998).
  3. Peter Vacher, "Johnny Parker Obituary", The Guardian (21 June 2010).

Hanyoyin Hadi na waje gyara sashe