Pamfir
Pamfir ( Ukraine) wani fim ne na almara na kasar Yukren wanda Dmytro Sukholitkyy-Sobchuk ya jagoranta, wanda aka fara haska ta ranar Mayu 22, 2022, a bikin 75th Festival de Cannes, a cikin zaɓi na Daraktoci 'Fornight 54. Ana rarraba shirin tun daga Maris 23, 2023. Daga Yuni 22 na wannan shekara, an saki fim din kafar Netflix . Fim ɗin ya sami babbar kyauta na bikin fina-finai na duniya na Alkahira, Grand Prix na Kyiv International Film Festival Molodist, ya shiga cikin bukukuwan fina-finai na duniya da yawa. An sanya sunan Pamfir a cikin mafi kyawun fina-finai na 2023 ta The Guardian.
Pamfir | |
---|---|
Asali | |
Lokacin bugawa | 2022 |
Asalin suna | Памфір |
Asalin harshe | Harshan Ukraniya |
Ƙasar asali | Ukraniya, Poland, Faransa da Chile |
Characteristics | |
Genre (en) | drama film (en) |
During | 100 Dakika |
Launi | color (en) |
Direction and screenplay | |
Darekta | Dmytro Sukholytkyy-Sobchuk (en) |
Marubin wasannin kwaykwayo | Dmytro Sukholytkyy-Sobchuk (en) |
'yan wasa | |
Tarihi | |
Nominations
| |
External links | |
Specialized websites
|
Oleksandr Yatsentiuk ya taka rawar tauraron shirin. An yi fim ɗin kafin Rasha ta mamaye kasar Yukren, kuma ya zama ɗaya daga cikin mahimman maganganun fasaha game da Yukren ta zamani - ruhun da ba ya karyewa da nufin rayuwa.
Labari
gyara sasheBabban jigon shirin, Pamfir, tsohon mai shigo da kayayyaki ne, amma mutumin kirki ne wanda ya koma ƙauyensa na haihuwa da ke yammacin Yukren, bayan ya yi aiki a ƙasashen waje tsawon shekaru da yawa. Ya tsai da shawara yin rayuwa ta gaskiya a yanzu, da haka ya kafa misali mai kyau ga ɗansa Nazar. Babban abubuwan da suka faru suna faruwa a Bukovina a jajibirin bikin gargajiya na Malanka . Amma a yankin, cin hanci da rashawa wani bangare ne na kowane fanni na rayuwa, kuma laifuka da addini suna da alaka da juna. Laifukan da aka shirya suna karkashin jagorancin Orest Ivanovych Mordovskiy, wanda ake yi wa lakabi da Morda ( Mug ), wanda kuma shi ne shugaban wani kamfanin kare gandun daji na gida. Kyakyawar rayuwa da Pamfir ke niyyan yin bashi yiwuwa, saboda wani abin da ya faru da ɗansa: Nazar yana so ya bar mahaifinsa a gida kuma ya ƙone takardunsa, kuma tare da su, ba da gangan ba, gidan addu'a. Yanzu, domin ya gyara barnar da aka yi, an tilasta wa Pamfir sake haɗuwa da abubuwan da ya faru a baya, ya koma aikata laifuka, ya zama memba na ƙungiyar masu laifi kuma ya sake yin fasa-kwari.
Tauraro
gyara sashe- Oleksandr Yatsentiuk - Leonid (Pamfir)
- Stanislav Potiak - Nazar, ɗan Leonid
- Solomiya Kyrylova - Olena, matar Leonid
- Olena Khoklatkina - mahaifiyar Leonid
- Myroslav Makovychuk - mahaifin Leonid
- Ivan Sharan - Viktor, kanin Leonid
- Oleksandr Yarema – Orest ( Morda )
- Andriy Kyrylchuk - Bobul, dan sanda
- Igor Danchuk – pastor Andriy
- Petro Chychuk - Vasyl, mai tsaron gida
- Vitaliy Boyuk - Kolya, tagwaye
- Oleksandr Boyuk - Tolya, tagwaye
- Kateryna Tysiak - Anhelina
- Viktor Baranovskiy - Shchur
- Halyna Sviata - mai tsaron iyakoki
- Heorhiy Povolotskiy – Bison, mai tsaron iyaka
- Oleksiy Leybiuk - Akela
- Volodymyr Lyutikov - mai tsaron iyaka
- Vitaliy Koval - Petro, mai tsaron iyakoki
- Zinoviy Symchych - firist
- Igor Demyanyuk
- Rymma Zyubina – Mai watsa shiri TV