Owunari Georgewill
Owunari Abraham Georgewill (an haife shi a ranar 15 ga watan Mayu 1965 [1] ) farfesa ne a fannin harhaɗa magunguna ɗan Najeriya kuma babban mataimakin shugaban jami'ar Fatakwal na 9th. [2][3]
Owunari Georgewill | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Abonnema, 15 Mayu 1965 (59 shekaru) |
Karatu | |
Makaranta | jami'ar port harcourt |
Sana'a | |
Sana'a | Malami |
Employers | jami'ar port harcourt (2021 - |
Rayuwar farko da asali
gyara sasheOwunari ya samu shaidar kammala karatunsa na farko a shekarar 1976 a makarantar Bishop Crowther Memorial, Abonnema. Ya rubuta jarabawar matakin O’Level a makarantar Nyemoni Grammar School, Abonnema a shekarar 1981 sannan a shekarar 1987 ya kammala karatunsa na jami’ar Fatakwal inda ya karanta ilimin haɗa magunguna sannan kuma ya yi digirinsa na biyu a makarantar.[1][4] He holds a bachelor of surgery and a Doctorate of Medicine in Pharmacology and Toxicology.[5] Ya yi digirin farko na tiyata da digirin digirgir a fannin likitanci da magunguna.
Sana'a
gyara sasheOwunari Georgewill ya fara koyar ne a matsayin malami na 2 a sashin ilimin haɗa magunguna na Jami'ar Fatakwal sannan ya zama shugaban tsangayar ilimin likitanci a shekarar 2010. Ya ci gaba kuma an ba shi mukamin Farfesa a fannin harhaɗa magunguna a ranar 4 ga watan Mayu, 2010, yana da shekaru 44. A 2012, an zaɓe shi mataimakin provost na Makarantar Kiwon Lafiya ta Jami'ar Fatakwal kuma a cikin shekarar 2013, an zaɓe shi a cikin Majalisar Gudanar da Jami'ar a matsayin wakili. A ranar 2 ga watan Yuli 2021, majalisar gudanarwar makarantar ta sanar da shi a matsayin mataimakin shugaban jami'a na 9 bayan tantance shi da wasu masu nema goma sha ɗaya.[6][7][2]
Rayuwa ta sirri
gyara sasheOwunari Georgewill ya auri Udeme Owunari Georgewill wacce associate farfesa ce kuma suna da ‘ya’ya huɗu da jika.
Manazarta
gyara sashe- ↑ 1.0 1.1 "Meet Owunari Abraham Georgewill, UniPort 9th Vice Chancellor". www.uniport.edu.ng. Retrieved 13 July 2022.[permanent dead link]
- ↑ 2.0 2.1 Chinedu, Clement (2 July 2021). "University of Port Harcourt gets new Vice Chancellor". Daily Post Nigeria (in Turanci). Retrieved 13 July 2022.
- ↑ https://independent.ng/uniport-alumni-felicitate-with-georgewill-as-9th-vc/
- ↑ "UNIPORT Alumni Felicitate With Georgewill As 9th VC". Independent Newspaper Nigeria (in Turanci). 6 July 2021. Retrieved 13 July 2022.
- ↑ "Georgewill's rich experience, unique credentials to lead UNIPORT". News Express Nigeria Website (in Turanci). Archived from the original on 1 February 2022. Retrieved 13 July 2022.
- ↑ "Georgewill Assumes Office As UniPort 9th VC As Okodudu Bows Out, Relives Experience". www.uniport.edu.ng. Archived from the original on 5 July 2022. Retrieved 13 July 2022.
- ↑ "UNIPORT governing council appoints VC". Punch Newspapers (in Turanci). 3 July 2021. Retrieved 13 July 2022.