Opay Digital Services Limited wanda aka fi sani da Opay, kuma tsohon Paycom Nigeria Limited, kamfani ne na fintech mai sarrafa kudi ta wayar hannu wanda Zhou Yahui ya kafa a 2013 mai hedikwata a Ikeja, Jihar Legas, Najeriya. Yana cikin manyan kamfanoni huɗu na fintech a Najeriya: Moniepoint Inc., Kuda, da PalmPay.[1]

Opay
kamfani
Logon Opay

Opay da aka sani da Paycom Nigeria Limited. An kafa ta a shekarar 2013, kuma babban bankin Najeriya ya ba shi lasisi a shekarar 2018. Kamfanin Inshorar Deposit na Najeriya ne ya ba shi inshora. A watan Mayun 2019, kamfanin Opay ya kaddamar da aiyukan sa na Point of sale, wanda akasari ya mamaye Najeriya yayin yajin aikin naira. A watan Nuwamba 2021 aka nada Olu Akanmu a matsayin babban jami'in Opay har sai ya yi murabus a 2023.[2]

A watan Mayun 2022, Opay Nigeria ta hada hannu da Verve International don yin rijistar katin cire kudi wato ATM. Opay ya tsawaita zuwa Masar a cikin 2021, kuma Babban Bankin Masar ya amince da shi tare da ba da katunan da aka riga aka biya. A cikin Satumba 2021, Opay ya sami tallafin ƙasa da ƙasa wanda bankin Soft ke jagoranta.

Abokan ciniki na Opay sun yi dandazo a hedkwatar kamfanin da ke Legas, kan sanarwar zamba daga wani wakili. A shekarar 2023 kotun shari’a a jihar Kano ta yanke wa wani wakilin Opay hukuncin daurin watanni tara a gidan yari bisa samunsa da laifin damfarar kudi ga wani abokin ciniki ta yanar gizo.

Manazarta

gyara sashe
  1. "Opay Digital Services Limited (Formerly Paycom Nigeria Limited)". Central Bank of Nigeria. Retrieved June 7, 2024.
  2. Solomon, Folu (May 8, 2024). "Nigeria: Opay, PalmPay face scrutiny amid rising appeal". The Africa Report.com. Retrieved June 7, 2024.