Oluwami Dosunmu-Ogunbi
Dan kasan American
Aiki Educator, Roboticist
Shahara akan First Black woman to obtain a PhD in Robotics
Title Robotics Engineer
Iyayes Dr Adedoyin Dosunmu Ogunbi (father)
Dr Sesi Dosunmu Ogunbi (mother)
Yanar gizo wamiogunbi.com

Oluwami Dosunmu-Ogunbi yar kasan Najeriya ne mazauniyar kasan Amurka, masanar harkan robots, injiniya ce, kuma malama. An san ta a matsayin mace baƙar fata ta farko da ta sami Ph.D. a cikin Robotics daga Jami'ar Michigan.[1][2][3][4]

Rayuwa da aiki

gyara sashe

Zuriya da tarihin ilimi

gyara sashe

An haifi Oluwami ga 'yan ci ranin iyayen na Najeriya, Adedoyin Dosunmu Ogunbi da Sesi Dosunmu Ugunbi . Mahaifin Oluwami ya kasance Daraktan Kiwon Lafiya ne a Duchess International Hospital dake cikin Legas, Najeriya kuma Mataimakin Farfesa a Jami'ar Alabama Birmingham[5][6]. Mahaifiyarta Sesi ta kasance ƙwararriyar likitan da ake wa lakabi da pediatric gastroenterology.[7][8]

Oluwami ta sami takardar shedar digirin ta na farko a fannin Injiniyanci daga Jami'ar Illinois Urbana-Champaign, a inda ta samu nasarar kammala karatu tare da karramawa a shekara ta 2017. Daga nan sai Oluwami ta ci gaba da karatu a Jami'ar Michigan Ann Arbor, inda ta samu takardar shedar digiri na biyu a fannin Injiniyanci a shekara ta 2020, sannan ta sami digiri na biyu (master's degree) da digiri na uku (Ph.D) a ilimin Robotics a shekara ta 2021 da 2024.[9][10][11][12]

Oluwami ta samu kanta a matsayin malaman dalibai a Jami'ar Michigan daga 2019 zuwa 2020. Ta kuma kasance Lead Engineering Learning Assistant na shirin Illinois Engineering First-Year Experience (IEFX) kuma ta rike matsayin Sand Casting Chair na Pi Tau Sigma, ƙungiyar girmama aikin injiniyanci. Kuma ta kasance mai nusarwa da ba da shawara ga ɗalibai kuma jagora a cikin Shirin Injiniyanci na Morrill, wanda ke mai da hankali kan karfafa ɗaliban injiniyan Afirka, Hispanic, da 'yan asalin Amurka.[13][14][15] A halin yanzun, Oluwami ta na rike da matsayin Mataimakiyar Farfesa Mai Ziyara a Sashen Mechanical Engineering a Cibiyar Fasaha ta Rose-Hulman. A ranar 6 ga Afrilun shekara ta 2024, an kaddamar da Oluwami cikin Edward Alexander Bouchet Graduate Honor Society (Bouchet Society), wanda aka masa suna a matsayin dan Afirka na farko da ya karbi digiri a Amurka (Physics, Jami'ar Yale, 1876). [16][17]

Wallafe-Wallafen limi

gyara sashe
  • Terrain-adaptive, alip-based bipedal locomotion controller via model predictive control and virtual constraints [18]
  • Stair climbing using the angular momentum linear inverted pendulum model and model predictive control [19]
  • Demonstrating a Robust Walking Algorithm for Underactuated Bipedal Robots in Non-flat, Non-stationary Environments [20]

Kyaututtuka

gyara sashe

Oluwami ta sami kyaututtuka da dama, fellowship da sauran karramawa, daga cikinsu su ne:

  • Karramawar Paul E. Parker (2016) [21]
  • Karramawar Mechanical Engineering Pi Tau Sigma MVP (2016) [22]
  • Karramawar Nasara ta Janet Eakman (2017) [23]
  • Rackham Merit Fellowship (2017)[24]
  • GEM Fellowship ( 2017) [25]
  • Karramawar Nasara na Willie Hobbs Moore (2022) [26]
  • Ford Foundation Pre-Doctoral Fellowship (Honourable Mention - 2022) [27]
  • Engineering Innovation Runner-Up in the 3 Minute Thesis Competition (2023) [28]
  • MLK Spirit Award for Mentoring and Inspiration (2024) [29]

Manazarta

gyara sashe
  1. "Meet Oluwami Dosunmu-Ogunbi, the First Black Woman to Earn PhD in Robotics from University of Michigan | Duchess International Magazine" (in Turanci). 2024-05-13. Retrieved 2024-08-27.
  2. "Oluwami Dosunmu-Ogunbi Makes History As The First Black Woman To Obtain A Ph.D. In Robotics At The University Of Michigan". Yahoo Tech (in Turanci). 2024-05-14. Retrieved 2024-08-27.
  3. Sanusi, Deborah (2024-05-08). "Nigerian emerges first black woman to bag PhD in Robotics at Michigan varsity". Punch Newspapers (in Turanci). Retrieved 2024-08-27.
  4. Ogunseyin, Oluyemi (2024-05-07). "Nigerian makes history as first Black woman to earn U-M Robotics PhD". The Guardian Nigeria News - Nigeria and World News (in Turanci). Retrieved 2024-08-27.
  5. "Duchess Executive Team". Duchess International Hospital (in Turanci). Retrieved 2024-08-27.
  6. "Adedoyin Bodunrin Oluyemisi DOSUNMU-OGUNBI personal appointments - Find and update company information - GOV.UK". find-and-update.company-information.service.gov.uk (in Turanci). Retrieved 2024-08-27.
  7. "Sesi Dosunmu-Ogunbi, M.D., F.A.A.P." USA Health (in Turanci). Retrieved 2024-08-27.
  8. "Dr. Sesi Dosunmu-Ogunbi, MD - Pediatric Gastroenterologist in Billings, MT | Healthgrades". www.healthgrades.com. Retrieved 2024-08-27.
  9. Communications, Grainger Engineering Office of Marketing and. "This undergrad has perfected the balancing act". mechse.illinois.edu (in Turanci). Retrieved 2024-08-27.
  10. Everett, Herman (2024-05-09). "Dosunmu-Ogunbi Becomes First Black Woman to Earn PhD in Robotics". TV360 Nigeria (in Turanci). Retrieved 2024-08-27.
  11. "About". Wami Ogunbi (in Turanci). Retrieved 2024-08-27.
  12. "Oluwami (Wami) Dosunmu-Ogunbi | Michigan Robotics". robotics.umich.edu (in Turanci). 2021-03-01. Retrieved 2024-08-27.
  13. "Meet Oluwami Dosunmu-Ogunbi, the First Black Woman to Earn PhD in Robotics from University of Michigan | Duchess International Magazine" (in Turanci). 2024-05-13. Retrieved 2024-08-27.
  14. Communications, Grainger Engineering Office of Marketing and. "Dosunmu-Ogunbi wins college leadership award". mechse.illinois.edu (in Turanci). Retrieved 2024-08-27.
  15. "Teaching". Wami Ogunbi (in Turanci). Retrieved 2024-08-27.
  16. tedxdet. "Speakers 2024". TEDxDetroit (in Turanci). Retrieved 2024-08-27.
  17. "About". Wami Ogunbi (in Turanci). Retrieved 2024-08-27.
  18. "Terrain-adaptive, alip-based bipedal locomotion controller via model predictive control and virtual constraints". scholar.google.com. Retrieved 2024-08-27.
  19. "Stair climbing using the angular momentum linear inverted pendulum model and model predictive control". scholar.google.com. Retrieved 2024-08-27.
  20. Dosunmu-Ogunbi, Oluwami; Shrivastava, Aayushi; Grizzle, Jessy W. (2024-03-04), Demonstrating a Robust Walking Algorithm for Underactuated Bipedal Robots in Non-flat, Non-stationary Environments, retrieved 2024-08-27
  21. "Honors & Awards". Wami Ogunbi (in Turanci). Retrieved 2024-08-27.
  22. Everett, Herman (2024-05-09). "Dosunmu-Ogunbi Becomes First Black Woman to Earn PhD in Robotics". TV360 Nigeria (in Turanci). Retrieved 2024-08-27.
  23. "Honors & Awards". Wami Ogunbi (in Turanci). Retrieved 2024-08-27.
  24. "Honors & Awards". Wami Ogunbi (in Turanci). Retrieved 2024-08-28.
  25. "Honors & Awards". Wami Ogunbi (in Turanci). Retrieved 2024-08-28.
  26. "Honors & Awards". Wami Ogunbi (in Turanci). Retrieved 2024-08-27.
  27. "Ford Foundation". ra.nas.edu. Retrieved 2024-08-27.
  28. "Honors & Awards". Wami Ogunbi (in Turanci). Retrieved 2024-08-27.
  29. "North Campus Deans' MLK Spirit Awards – Office of Culture, Community and Equity (OCCE)". culture.engin.umich.edu. Retrieved 2024-08-27.