Olufunke Adeboye 'yar Najeriya ce kuma farfesa ce a fannin Tarihin Zamani a Sashen Tarihi da Dabarun Nazari na Jami'ar Legas, Najeriya. Marubuciya ce dake da lambar yabo, ita ce mai rike da mukamin shugabancin Tsangayar Fasaha na Jami'ar Legas. A shekarar 2013 ta lashe lambar yabo ta Gerti Hesseling da AEGIS (Africa-Europe Group for Interdisciplinary Studies) don kyawun mukalar da ta rubuta wanda wani masanin Afirka ya wallafa a mujallar Nazarin Afirka ta Turai.

Olufunke Adeboye
Rayuwa
Karatu
Makaranta Jami'ar Ibadan
Sana'a
Sana'a Masanin tarihi
Employers Jami'ar jahar Lagos
Wannan Muƙalar guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.

Tarihin Rayuwa

gyara sashe

An haifi Olufunke Adeboye (née Òjó) a garin Ibadan, Najeriya. Ta kammala makarantar sakandare a makarantar 'Our Lady's High School', Ile-Ife, Jihar Osun, Najeriya a shekarar 1983. Ta ci gaba zuwa Jami'ar Ibadan, Najeriya inda ta sami digiri na farko na Arts (BA), digiri na biyu (MA), da digirin digirgir (PhD.) A Tarihi a cikin shekarar 1988, 1990, da 1997 bi da bi. Ta fara aikin koyarwa ne a matsayin Mataimakiyar Malama a Jami’ar Jihar Ogun (a yanzu ta zama Jami’ar Olabisi Onabanjo ), Ago Iwoye, Najeriya a shekarar 1991. A shekarar 1999, ta kuma tsallaka zuwa sashen tarihi na jami’ar Legas na wancan lokacin a matsayin Malama mai daraja ta I, inda matsayinta yayi ta ƙaruwa har aka ayyana ta a matsayin cikakkiyar Farfesa a watan Maris din shekarar 2011.

Zaɓaɓɓun wallafe-wallafe

gyara sashe
    • “Framing Female Leadership on Stage and Screen in Yorubaland: Efunsetan Aniwura Revisited”, Gender & History 30, no.3, (October 2018): 666-681. https://doi.org/10.1111/1468-0424.12396
    • “Explaining the Growth and Legitimation of the Pentecostal Movement in Africa”, in Adeshina Afolayan, Jumoke Yacob-Haliso and Toyin Falola (eds.), Pentecostalism and Politics in Africa (Cham, Switzerland: Palgrave Macmillan, 2018), 25-40. https://www.palgrave.com/gp/book/9783319749105
    • “Home Burials, Church Graveyards and Public Cemeteries: Transformation in Ibadan Mortuary Practice, 1853-1960”, Journal of Traditions and Beliefs (Cleveland State University, Ohio, USA), 4 (2016) https://engagedscholarship.csuohio.edu/cgi/viewcontent.cgi?article=1060&context=jtb
    • "‘A Church in a Cinema Hall?’: Pentecostal Appropriation of Public Space in Nigeria," Journal of Religion in Africa 42, no. 2 (2012): 145-171. https://doi.org/10.1163/15700666-12341227
    • Adeboye, O. “Reading the Diary of Akinpelu Obisesan in Colonial Africa”, African Studies Review 51, no. 2 (2008): 75-97. https://doi.org/10.1353/arw.0.0074
    • “‘Iku Ya J’Esin’: Politically Motivated Suicide, Social Honor and Chieftaincy Politics in Early Colonial Ibadan”, Canadian Journal of African Studies 41, no. 2 (2007): 189-225. https://doi.org/10.1080/00083968.2007.10751356
    • “The Changing Conception of Elderhood in Ibadan, 1830-2000”, Nordic Journal of African Studies 16, no. 2 (2007): 261-278. https://njas.fi/njas/article/view/70/63
    • “Arrowhead of Nigerian Pentecostalism: The Redeemed Christian Church of God, 1952-2004”, Pneuma: Journal of the Society of Pentecostal Studies 29, no. 1 (Spring 2007): 23-56. https://doi.org/10.1163/157007407X178238
    • “Diaries as Cultural and Intellectual Histories” in Toyin Falola and Ann Genova (eds.), Yoruba Identity and Power Politics (Rochester, NY: University of Rochester Press, 2006), 74-95. JSTOR, https://www.jstor.org/stable/10.7722/j.ctt81p3p/8-Adeboye Archived 2020-08-06 at the Wayback Machine

Manazarta

gyara sashe