Olufemi Onabajo
Olufemi Onabajo masanin ilimin Najeriya ne, farfesa kuma tsohon mataimakin shugaban jami'ar Lead City, jami'a mai zaman kanta a Najeriya.[1]
Olufemi Onabajo | |
---|---|
Rayuwa | |
ƙasa | Najeriya |
Karatu | |
Makaranta | Jami'ar jahar Lagos |
Sana'a | |
Sana'a | Malami |
Sana'a
gyara sasheOnabajo ya fara aikinsa a matsayin malamin sakandare tun a shekarar 1978.[1] Ya yi aiki a matsayin edita a kamfanin yada labarai na jihar Ogun (OGBC).[1] Ya yi karatu kuma an ba shi digiri na biyu a Jami’ar Legas. Daga nan ya shiga gidan talabijin na Najeriya NTA da ke Ikeja, inda ya yi aiki na tsawon shekaru 10 kafin ya zama mai kula da labarai da al’amuran yau da kullum. Ya rubuta litattafai 23 a fannin sadarwar jama’a.[1]