Olu Ginuwa II ya kasance mai rike da sarautar gargajiya na Najeriya kuma babban jigo na Itsekiri wanda shine Olu wato sarki na Warri daga 1936 zuwa 1949.[1] Shi ne Olu na Masarautar Warri na 17 mai suna Ogiame Ginuwa II. An haife shi a garin Emiko Ikengbuwa. Ya gaji kakansa, Olu Akengbuwa a matsayin Olu na Warri bayan da aka shafe shekaru 88 ana gudanar da harkokin siyasar Warri a karkashin mulkin ‘yan kasuwa. Atsibutsere Skinn, dan Gimbiya Agbeje Ikengbuwa, shi ne ya jagoranci zabe da kuma nada Ogiame Ginuwa II a shekarar 1936 a matsayin shugaban gidan sarauta.[2]

Olu Ginuwa II
Rayuwa
Haihuwa Najeriya
Sana'a
Wannan Muƙalar guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.


Manazarta

gyara sashe
  1. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2022-08-21. Retrieved 2024-09-07.
  2. https://www.worldcat.org/oclc/179792923