Olakunle Oluomo
Olakunle Taiwo Oluwabukunmi Oluomo (an haife shi 11 Oktoba 1963)[1] ɗan siyasan Najeriya ne a halin yanzu yana aiki a matsayin ɗan majalisar dokokin jihar Ogun. Ya rike mukamin kakakin majalisar dokokin jihar Ogun ta 9 daga shekarar 2019 zuwa 2023 sannan kuma aka sake zabe shi a matsayin kakakin majalissar ta 10 a watan Yunin 2023 har zuwa watan Janairun 2024 inda aka tsige shi bisa zargin almubazzaranci da kudade.
Olakunle Oluomo | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | 1963 (60/61 shekaru) |
Sana'a | |
Sana'a | ɗan siyasa |
Siyasa
gyara sasheAn zabe shi ne a karo na 7 a majalisar dokokin jihar Ogun a shekarar 2011 a kan tikitin jam’iyyar Action Congress of Nigeria (CAN) don wakiltar mazabar jihar Ifo 1.[2] Ya yi aiki a matsayin shugaba, kwamitin majalisar kan harkokin kananan hukumomi da masarautu da mataimakin shugaban kwamitin majalisar kan shari’a, da’a da kuma koken jama’a. A shekarar 2015 ne aka sake zabe shi a majalisa ta 8 a kan tikitin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) bayan hadewar ACN da wasu jam’iyyun adawa da suka kafa APC. An zabe shi a majalisa ta 9 a shekarar 2019 kuma ya zama kakakin majalisar a tsawon zaman (2015-2023). Bayan sake zabensa a shekarar 2023, an sake zabe shi a matsayin kakakin majalisa ta 10 kuma ya yi aiki har zuwa watan Janairun 2024 lokacin da aka cire shi daga mukaminsa kan zargin almubazzaranci da kudade.