Ogoh Odaudu (an haife shi 3 ga Agustan shekarar 1981) ɗan wasan ƙwallon kwando ne na Najeriya mai ritaya kuma koci na yanzu. A halin yanzu shi ne babban kocin Rivers Hoopers na gasar Premier ta Najeriya. A shekarunsa na taka leda, Odaudu ya kasance ɗan wasan ƙungiyar ƙwallon ƙwando ta Najeriya.[1]

Ogoh Odaudu
Rayuwa
Haihuwa Jos, 1981 (42/43 shekaru)
Sana'a
Sana'a basketball coach (en) Fassara da basketball player (en) Fassara
Itinerary
Ƙungiyoyi Shekaru Pos Nbr
 

Sana'ar wasa

gyara sashe

An haife shi a garin Jos, ya buga wa ƙaramar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Najeriya wasa a gasar FIBA ta ƴan ƙasa da shekaru 19 a shekarar 1999.

Odaudu ya kuma kasance memba a babban tawagar Najeriya kuma ya taka leda a gasar cin kofin Afrika ta FIBA a shekarar 2001, 2003. Ya kuma taka leda a Gasar Commonwealth ta 2006.

Aikin koyarwa

gyara sashe

Odaudu ya kasance babban kocin Rivers Hoopers tun lokacin da aka kafa ƙungiyar a shekarar 2009, Ya horar da ƙungiyar zuwa gasar Premier har sau uku. Don haka ƙungiyar ta samu gurbin shiga gasar BAL ta shekarar 2021 inda ya horar da su a gasar farko. Tun a shekarar 2019, Odaudu ya kasance mataimakin kocin tawagar ƙwallon ƙafan Najeriya. Ya kasance mataimakin koci a gasar Olympics ta 2020 a Tokyo. Odaudu ya kasance babban kocin Najeriya a AfroCan 2019.[2]

Manazarta

gyara sashe
  1. "Ogoh Odaudu's profile". FIBA.basketball. Retrieved 25 September 2021.
  2. Cite error: Invalid <ref> tag; no text was provided for refs named bal