Ofishin Kula da Bashi (Najeriya)
Ofishin kula da basussuka ( DMO ) hukuma ce ta gwamnati da aka kafa ta a ranar 4 ga watan Oktoba,shekara ta 2000, wacce ke da alhakin karkatar da basussukan Najeriya.[1] An ƙirƙiro ta ne saboda ƙalubalen da ke tattare da tsarin basussukan Najeriya, waɗanda suka haɗa da dimbin basussuka na waje da na cikin gida, dimbin basussuka, ƙarancin ajiyar waje, da rashin karfin sarrafa basussukan.[1]
Ofishin Kula da Bashi | |
---|---|
Bayanai | |
Iri | government agency (en) |
Ƙasa | Najeriya |
Tarihi | |
Ƙirƙira | 4 Oktoba 2000 |
dmo.gov.ng |
Tarihi
gyara sasheAn kafa hukumar DMO ne biyo bayan shawarwarin da sashin Kula da abashi (DMD) na susun Ba da Lamuni na Duniya (IMF) ya bayar bayan wani cikakken nazari kan yanayin basussukan Najeriya a cikin shekara ta 1999.[2][3] (DMD) ta ba da shawarar kafa hukuma guda ɗaya da ke da alhakin duk abubuwan da suka shafi kula da basussukan jama'a, gami da tsara manufofi, haɓaka dabaru, rance, rikodi, sabis, da bayar da rahoto.[3]
Da farko wani ɓangare ne mai cin gashin kansa a cikin Fadar Shugaban ƙasa, daga baya aka mayar da (DMO) zuwa Ma'aikatar Kudi a cikin shekara ta 2001 kuma an inganta shi zuwa cikakkiyar parastatal a cikin shekara ta 2003.[4] Tsarin doka don aikin (DMO) ya haɗa da Dokar Nauyin Kuɗi na 2007 da Dokar Kafa hukumar ta (DMO) a cikin shekara ta 2003.
Ayyuka
gyara sasheBabban ayyuka na (DMO) shine ba da shawara ga Gwamnatin Tarayya game da kula da basussukan jama'a, tara kuɗi ta hanyar gida da waje, kula da cikakkun bayanai na basussukan jama'a, hidimar duk basussukan jama'a,[4] sarrafa haɗarin da ke tattare da shi, haɓaka bashi. dabarun gudanarwa, inganta kasuwar bashi na cikin gida, da haɗa kai da masu ruwa da tsaki kan al'amuran kula da basussukan jama'a.[4]
Ƙungiya
gyara sasheHukumar ta (DMO) dai na ƙarƙashin jagorancin Darakta-Janar ne, wanda shugaban ƙasa ya naɗa na tsawon shekaru biyar, tare da yiyuwar sabunta wasu shekaru biyar.[5] Daraktocin Zartarwa guda uku suna kula da sassan aiki na hukumar (DMO): Ci gaban Kasuwa, Gudanar da Fayiloli, da Dabarun Manufofi da Gudanar da kaucewa haɗari. Bugu da ƙari, akwai sassan wasu ayyukan guda huɗu: Aikin gaba-daya, Binciken Ciki, Ayyukan Shari'a, da Harkokin Jama'a.[6] Hukumar ta (DMO) na aiki ne ta ofisoshin shiyyoyi shida da ke yankuna daban-daban don daidaita tsarin kula da basussuka a matakin jiha da ƙananan hukumomi.[5]
Nasarorin da aka samu
gyara sasheHukumar (DMO) ta samu gagarumin ci gaba ta hanyar rage yawan basussukan da Najeriya ke samu a waje,[7] ƙara yawan ajiyar waje,[8] inganta kimar kiredit,[9] bayar da lamuni mai nasara na ƙasa da ƙasa (Eurobonds, Sukuk bonds, and Green Bonds),[10][11][12] da ƙarfafa dabarun sarrafa bashi. Ta inganta karfin masu kula da basussukan jama'a, samar da ilimi kan kula da basussukan jama'a, da kiyaye rahotanni akai-akai don wayar da kan jama'a.
Ƙalubale
gyara sashe(DMO) na fuskantar ƙalubale da suka shafi gudanar da hajojin bashin jama'a da ke tasowa,[13] tsadar ayyukan bashi na cikin gida, raguwar rabon bashi na waje, buƙatar daidaitawa da daidaitawa a cikin kula da bashi, ingantawa a cikin tsarin shari'a da hukumomi, da kuma tabbatar da gaskiya da riƙon amana.[14]
Manazarta
gyara sashe- ↑ 1.0 1.1 "Debt Management Office (Nigeria)". Devex. Retrieved 28 October 2023.
- ↑ "About DMO". About DMO. 2 October 2023. Retrieved 28 October 2023.
- ↑ 3.0 3.1 Counterparty., Another (21 March 2001). "Guidelines for Public Debt Management". IMF. Retrieved 28 October 2023.
- ↑ 4.0 4.1 4.2 "debt management office establishment (etc.) act 2003". Retrieved 28 October 2023.
- ↑ 5.0 5.1 "President Buhari Appoints Patience Oniha as DG DMO – The Statehouse, Abuja". The Statehouse, Abuja. 30 June 2022. Retrieved 28 October 2023.[permanent dead link]
- ↑ "Buhari Approves Reappointment of Patience Oniha as DG of DMO". Lawyard. 30 June 2022. Retrieved 28 October 2023.
- ↑ "Nigerian Debt Relief". Center For Global Development. 21 April 2006. Retrieved 28 October 2023.
- ↑ "External Reserves Accumulation and the Estimation of the Adequacy Level for Nigeria" (PDF). Retrieved 28 October 2023.
- ↑ "Fitch Assigns Nigeria 'BB-' Rating; Outlook Stable". Fitch Ratings. Retrieved 28 October 2023.
- ↑ Ugbodaga, Mary (28 January 2021). "Nigeria redeems its first-ever 10-year $500m Eurobond". TheCable. Retrieved 28 October 2023.
- ↑ "Nigerian govt releases N100 billion Sukuk Bond proceeds for 25 Road Projects". Premium Times Nigeria. Retrieved 28 October 2023.
- ↑ "Sukuk Some Highlights of the N100 Billion Sovereign Sukuk". Debt Management Office Nigeria. 2 October 2023. Retrieved 28 October 2023.
- ↑ "National Debt Management Framework 2008". Debt Management Office Nigeria. 2 October 2023. Retrieved 28 October 2023.
- ↑ Yusuf, Abdulkarim; Mohd, Saidatulakmal (1 January 2021). "The impact of government debt on economic growth in Nigeria". Cogent Economics & Finance. Informa UK Limited. 9 (1). doi:10.1080/23322039.2021.1946249. hdl:10419/270116. ISSN 2332-2039.