Noor Deen Mi Guangjiang
Haji Noor Deen Mi Guangjiang (an haife shi a 1964) ƙwararren mai zane ne salon addinin Islama, ƙwararre kan salon Sini wanda ya samo asali daga al'adun Musulmin China.
Noor Deen Mi Guangjiang | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Shandong (en) , 1963 (61/62 shekaru) |
Sana'a | |
Sana'a | calligrapher (en) |
An haife shi a lardin Shandong, malami ne a Kwalejin Musulunci da ke Zhengzhou a lardin Henan, sannan kuma mai bincike ne kan al'adun Musulunci a Kwalejin Kimiyya ta Henan. A cikin 1997, Haji Noor Deen shine Musulmin China na farko da aka ba wa Takaddar Karatun Larabci na Masar kuma aka shigar da shi memba na Ƙungiyar Kira na Masarr. An san shi da yin ƙayatattun zanuka.