Nasiru L. Abubakar
Nasiru L. Abubakar ɗan jarida ne ɗan Najeriya daga Kaduna kuma Editan Kamfanin Dateline Nigeria, wani kamfani da ke yada labaran A intanet da ke Abuja, Najeriya .[1] [2][3]
Nasiru L. Abubakar | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | 4 Satumba 1977 (47 shekaru) |
Sana'a | |
Sana'a | ɗan jarida |
Farkon Rayuwarshi
gyara sasheAn haifi Nasiru a ranar huɗu 04 ga Satumba, shekarar alif dubu ɗaya da ɗari tara da saba'in da bakwai 1977,[4] a karamar hukumar Kaduna ta Arewa a jihar Kaduna . Nasiru ya yi PGD a Mass Communication daga BUK, PGD a fannin hulda da kasashen duniya da diflomasiyya baya ga HND a Mass Communication da yayi a Kaduna Polytechnic Kaduna.[5]
Aikin Jarida
gyara sasheNasiru ya fara aikin jarida ne a ABG Group. Ya yi aiki na ɗan lokaci a matsayin mai horarwa da KSMC da ke Kaduna kafin ya fara shiga jaridar Daily Trust a matsayin mai zaman kansa a watan Agusta, shekarar alif dubu biyu 2000 kafin ya zama ma’aikaci na dindindin a shekarar alif dubu ɗaya biyu da huɗu 2004.[6] [7] A Aminiya, an nada shi Editan riko (Asabar) a shekarar alif dubu biyu da goma Sha biyu 2012, kafin a mayar da shi Daily Trust a matsayin Mataimakin Edita. A cikin shekarar alif dubu biyu da goma Sha hudu 2014 kafin a tabbatar da shi a matsayin edita a shekarar 2016. A matsayinsa na edita, ya lashe kyautar Gwarzon Jarida a shekarar alif dubu biyu da goma Sha shida 2016 kuma Aminiya ta lashe kyautar Jarida ta bana.
A shekarar 2019, Nasiru ya zama Manajan Editan Daily Trust. Ya yi murabus a shekarar alif dubu biyu da ashirin 2020 ya koma Dateline Nigeria a matsayin Babban Editan.
Manazarta
gyara sashe- ↑ "Daily Trust Appoints New Editors". PR Nigeria. 2 September 2019.
- ↑ "New appointments at Trust Newspapers". mediacareerng.org. 1 February 2016.
- ↑ "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2022-06-24. Retrieved 2023-11-25.
- ↑ https://www.apollo.io/people/Nasiru/Lawal/54ebcc6a74686943114bc027/
- ↑ https://www.blueprint.ng/kaduna-train-attack-abductors-release-photos-families-identify-captives/
- ↑ https://allafrica.com/stories/200905110970.html
- ↑ https://allafrica.com/stories/200908040443.html