Nadeen Ashraf
Nadeen Ashraf (Larabci: نادين اشرف; an haife ta ranar 12 ga watan Maris 1998) ƴar gwagwarmayar mata ce ta Masar.[1]
Nadeen Ashraf | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Kairo, 12 ga Maris, 1998 (26 shekaru) |
ƙasa | Misra |
Harshen uwa | Egyptian Arabic (en) |
Karatu | |
Makaranta | Jami'ar Amurka a Alkahira |
Harsuna |
Larabci Egyptian Arabic (en) |
Sana'a | |
Sana'a | Mai kare hakkin mata |
Kyaututtuka |
gani
|
Mamba | MeToo movement (en) |
Tarihin rayuwar ta
gyara sasheAn haifi Ashraf ta a birnin Alkahira a shekara ta 1998. Mahaifinta mawallafin abubuwan da suka shafi software ne kuma mahaifiyarta tana sana'ar saida abinci Tun daga shekarar 2020, tayi karatun Falsafa da Kimiyyar Siyasa a Jami'ar Amurka da ke Alkahira. A daren ranar 1 ga Yuli, shekarar 2020, Ashraf ta buɗe wani shafin asusun Instagram mai suna "Assault Police", wanda shine dandalin jama'a na farko don baiwa matan Masar damar yin murya a cikin ƙasar na #MeToo. A cikin ƙuri'ar jin ra'ayin jama'a ta shekarar 2013, kashi 99% cikin 100 na matan Masar sun ce sun tsira daga cin zarafi ta dalilin shirye-shiryen ta.
Ashraf ce ta buɗe shafin "Assault Police" na Instagram da farko don samar da wata kafa ga matan da suka fuskanci cin zarafi da fyade don bayyana abubuwan da suka faru a fili. Asusun ya taka rawar gani wajen bankado lamarin wanda ake zargi da aikata fyade, Ahmed Bassam Zaki, wanda aka yanke masa hukuncin daurin shekaru uku a gidan yari saboda laifin cin zarafi ta yanar gizo a watan Disamba 2020. Wannan babban al'amari ya sa manyan jami'ai da ƙungiyoyi a ƙasar Masar, irin su Masallacin Al-Alzhar na Alƙahira, suka yi magana game da fyaɗe da cin zarafi. Abubuwan da ke cikin akkawunt na "Assault Police" sun bayyana yadda ake faɗaɗa ɓarna haka ta bayyana damuwar ta game da yadda ake cin zarafin mata, haka kuma ta bada shawarar a dinga ilmantarws da samar da kayan aiki ga mata don suma a dama dasu. Har ila yau, ta ƙirƙira wasu ƙungiyoyi tare da ƙarfafa wasu mata su yi magana game da cin zarafi da akewa mata, kamar ɗalibai a Cibiyar Fina-Finai ta Masar.
Kyaututtuka
gyara sasheA shekarar 2020, Ashraf ta kasance daya daga cikin shahararrun mata 100 na BBC. An kuma ba ta lambar yabo ta Changemaker a Equality Now Virtual, wanda Gucci ke ɗaukar nauyinta.[2][3][4]
Manazarta
gyara sashe- ↑ Farouk, Menna A. (2020-09-03). "Egypt's #MeToo crusader fights sex crimes via Instagram". Reuters (in Turanci). Retrieved 2021-01-06.
- ↑ "BBC 100 Women 2020: Who is on the list this year?". BBC News (in Turanci). 2020-11-23. Retrieved 2021-01-06.
- ↑ "BBC names two Egyptians in its '100 Women 2020' list". Egypt Independent (in Turanci). 2020-11-24. Retrieved 2021-01-06.
- ↑ "Egyptian Activist Nadeen Ashraf Honored by Equality Now Among International Public Figures". Egyptian Streets (in Turanci). 2020-12-04. Retrieved 2021-01-06.