Mutuwar Vincent van Gogh, mai zane ɗan kasar Holand, ya faru ne da sanyin safiyar ranar 29 ga watan Yulin 1890, a cikin ɗakinsa a Auberge Ravoux a ƙauyen Auvers-sur-Oise a arewacin Faransa. Kwanaki biyu kafin nan, Van Gogh ya harbe kansa ko kuma da gangan wani ya harbe shi. Yayin da takardar shaidar mutuwarsa ta bayyana cewa ya mutu ne a dalilin cewa ya kashe kansa, akalla wasu masu rubuta tarihin rayuwa su biyu sun kalubalanci hakan, inda suka ce mai yiwuwa wani ne ya harbe shi da gangan.

Infotaula d'esdevenimentMutuwar Vincent van Gogh
Iri Mutuwa

Tushen labari

gyara sashe
 
Ward a Asibiti a Arles, Vincent van Gogh (1889)

Bayyanar farko-farko na mutuwarsa

gyara sashe

A farkon shekarar 1883, Vincent van Gogh ya rubuta wa ɗan'uwansa Theo : "... Game da lokacin da har yanzu ina da damar yin ayyuka na nan gaba, ina tsammanin jikina zai riƙe ni na zuwa wasu adadin shekaru. .. tsakanin 7-10, ya ce", ". . . Ya kamata in shirya tsawon tsakanin shekaru 5 zuwa 10. . " [1] Jami'in Van Gogh Ronald de Leeuw ya ayyana wannan batu da cewa "ya rubuta a wannan ne saboda yana tunanin cewa zai shawa kan matsalolinsa a tsakanin shekaru goma".

Wannan Muƙalar guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.


Manazarta

gyara sashe
  1. Vincent van Gogh, "letter to Theo van Gogh, written c. 4-8 August 1883 in The Hague", translated by Johanna van Gogh-Bonger, edited by Robert Harrison, letter number 309.