Nasiru Sule Garo
An haifi Hon Nasiru Sule Garo a ranar 28 ga watan Janairun 1974 a Garin Garo, Karamar Hukumar Kabo ta Jihar Kano, Najeriya. Ya wakilci karamar hukumar Gwarzo/kabo a majalisar wakilai ta tarayya.
Hon. Nasiru Sule Rayuwar Farko
Hon Nasiru ya halarci Makarantar Firamare ta Garo ta Tsakiya inda ya samu takardar barin Makarantar Farko (FSLC). Ya yi karatun sakandare a Makarantar Sakandaren Garo Junior da Kwalejin Fasaha ta Bagauda inda ya sami Babban Takaddar Shaida ta Yammacin Afirka (WASC). Ya halarci Jami'ar Bayero ta Kano kuma ya sami Diploma a fannin sadarwa, Advance Diploma management information da kuma digiri na farko a kimiyyar siyasa.
Kafin shiga siyasa, Hon Nasiru ma’aikacin Garo Tannery Kano da Trends Venerate Ltd Kano ne. Daga 2002 zuwa 2003 ya kasance mataimaki na musamman ga Maigirma Gwamnan Jihar Kano.
A shekarar 2007 an zabe shi a majalisar wakilai a karkashin jam'iyyar People's Democratic Party (PDP) don wakiltar mazabar Gwarzo/kabo. An sake zabensa a 2011.
Daga 2011 zuwa 2015 ya yi aiki a cikin kwamitoci masu zuwa; Albarkatun Man Fetur (Down Stream), Sufurin kasa, Tsaron Ruwa, Ilimi & Gudanarwa, Magunguna, da Ci gaban Birane & Tsarin Yanki.
An sake zabensa a karo na uku a 2015 a karkashin jam'iyyar All Progressive Congress (APC). Yana kuma aiki a matsayin Mataimakin Shugaban Kwamitin Siyarwa na Jama'a.
<\https://citizensciencenigeria.org/public-offices/persons/nasiru-sule-garo/>