Adamu Chiroma

Sake dubawa tun a 16:33, 1 ga Augusta, 2021 daga Mr. Sufie (hira | gudummuwa) (Sabon shafi: An haife shi a shekarar 1934 a garin Pika da ke cikin tsohuwar jahar Borno, yanzu kuma ya koma jahar Yobe. Karatu 1943 - 1947: Makarantar elimantare ta Pika daga baya kuma ya koma Potiskum. 1947 - 1949: Makarantar midil ta Borno da ke Maiduguri. 1950 – 1955: Kwalejin Barewa da ke Zariya. 1955 – 1958: Nigerian College of Art Zaria, wacce yanzu ta koma ABU. 1958 – 1961: Jami’ar Ibadan (Ibadan University) inda ya yi karantun digiri a fannin tarihi (Bachelor of History). G...)
(bamban) ←Canji na baya | Zubi na yanzu (bamban) | Canji na gaba → (bamban)
An haife shi a shekarar 1934 a garin Pika da ke cikin tsohuwar jahar Borno, yanzu kuma ya koma jahar Yobe.

Karatu 1943 - 1947: Makarantar elimantare ta Pika daga baya kuma ya koma Potiskum. 1947 - 1949: Makarantar midil ta Borno da ke Maiduguri. 1950 – 1955: Kwalejin Barewa da ke Zariya. 1955 – 1958: Nigerian College of Art Zaria, wacce yanzu ta koma ABU. 1958 – 1961: Jami’ar Ibadan (Ibadan University) inda ya yi karantun digiri a fannin tarihi (Bachelor of History). Gogayyar Aiki “A lokacin duk wanda ya je makaranta ana jiransa da aiki, saboda haka ina fitowa sai aka bani aiki a ofishin Sardauna, inda na yi aiki na tsawon shekaru biyu. Daga baya kuma aka yi min DO (District Officer) a Mambila da kuma Lardin Sardauna (Sardauna Province); wannan lardi ta haɗa da Mubi, Goza, Ganye, da kuma Mambila. Sai dai, Mubi ita ce Helikwatar wannan lardi; Ganye da Mubi su ne Lardin Sardauna, amma da can baya, a cikin Kamaru (Cameroon) suke, Marigayi Sir Ahmadu Bello Sardauna ne ya yi ƙoƙari suka dawo Najeriya, saboda haka ake kiransu da sunansa, wato Lardin Sardauna (Sardauna Province)”. Marigayi Alhaji Adamu Ciroma (2017). Sai kuma a cikin shekarar 1965 ya koma zuwa gwamnatin tarayya da aiki, inda aka tura shi hukumar kula da ma’aikata (civil service). Suna cikin wannan aiki sai aka yi juyin mulkin 1966. A wannan guri ya yi aiki da Federal Ministry of Mines and Power (Lokacin Marigayi Ɗanmasanin Kano ne Ministan Ma’aikatar). Yana cikin wannan aiki sai gwamnatin Arewa ta kafa Jarida mai suna New Nigerian Newspaper. Sai aka yi masa Editan farko na wannan kamfanin jarida. Bayan edita ya riƙe janaral manaja, sai kuma manajan darekta na wannan kamfani. “Kamar yadda aka sani, gwamnoni suna son a yi abu yadda suke so, ni kuma ina son yin abu bisa doka da ƙa’ida da bin gaskiya, saboda haka sai muka samu saɓani da gwamnonin Arewa a lokacin, abin da ya haifar da bari na aiki kenan a wannan kamfani na jarida”. Sai kuma daga baya ya koma kamfanin masaƙa na United Nigerian Textile. Ya yi aiki a wannan kamfani na tsawon shekara biyu. Sai kawai aka yi juyin mulki na Murtala. Haka nan kuma a lokacin da yake kamfanin New Nigerian Newspaper, ya riƙe muƙamin darakta a Babban Banki Najeriya har zuwa ƙarshen zamansa na textile. Sannan kuma bayan juyin mulkin sojojin na farko, an zaɓe shi a matsayin wakili mai wakiltar Borno, zaɓen da aka yi shi ba tare da saninsa ba, sai dai kawai an sanar da shi cewa ya je Lagos don wakiltar jaharsa ta Barno a wajen taron sake tsara Kundin Mulkin Najeriya wanda aka kammala shi a shekarar 1979. “Muna tsaka da wannan aiki na tsarin mulki, sai maganar siyasa ta shigo ciki, saboda mutane suna cewa idan aka yi wannan tsarin mulki su waye za su gudanar da shi? Saboda haka a wannan zama aka kafa jama’iyyun siyasa da suka haɗa daNPN, PRP, da sauransu”. Bayan an kafa waɗannan jama’iyyu sai aka yi zaɓen da ya ɗora Alhaji Shehu Shagari a kan mulki. Alhaji Adamu Chiroma yana daga cikin waɗanda aka zaɓa don su tsaya takarar shugabanci ƙasa daga Arewa. Sunan sa shi ne na uku a wajen babban taron NPN da aka yi a Lagos (Convention). Bayan da aka kai waɗannan sunaye Lagos, sai wasu ‘yan arewa suka ce basu yarda ba suma sai an saka sunansu. Daga irin waɗannan mutane akwai Bukola Saraki, da Iya Abubakar. Faruwar wannan sai aka ce to a sake zaɓe. Da aka sake zaɓe sai da aka sake saka sunayensu su uku da farko sannan kuma aka ƙara sunayen mutane uku. Bayan wannan kuma sai aka sake buga zaɓe. A karon farko sai aka sake watsar da waɗancan ukun aka sake fitar da ukun farko. Daga nan kuma sai aka shiga yarjejeniyar musamman tsakanin mutanen Barno da Kano. A wannan sulhu aka ce idan aka sake gudanar da wannan zaɓe na fitar da gwani kuma aka dace aka fitar da gwani guda ɗaya, akwai yiwuwar samun matsala, saboda haka sai shi Chiroma da Ɗanmasanin Kano suka janye wa Shagari. Saboda haka daga baya sai aka naɗa Adamu Chiroma ya zama sakataren jama’iyya, shi kuma Alhaji Shehu Shagari ya zama ɗantakara. Daga nan sai aka shiga hidimar kamfe, inda bayan an kaɗa zaɓe sai Shagari ya ci zaɓe. Gwamnan Babban Bankin Najeriya Bayan da ya bar aiki a New Nigerian Newspaper, gwamnati ta naɗa shi ya zama darakta na Babban Bankin Najeriya (CBN). Muƙamin da ya riƙe tsawon shekaru biyu. Alhaji Adamu Chiroma Hoto Jaridar Vanguard Barin Aiki da Shiga Siyasa Alhaji Adamu Chiroma ɗan siyasa ne tun daga jamhuriya ta farko. A jamhuriyar farko ya yi jama’iyyar NPC, jamhuriya ta biyu kuma da shi aka kafa jama’iyyar NPN, sai kuma jamhuriya ta huɗu da aka kafa jama’iyyar PDP da shi. Alhaji Adamu Chiroma ya ce, “Ina cikin riƙe da wannan kujera, sai na samu saƙo daga jahata ta Barno cewa an zaɓe ni na wakilci Barno a wajen taron Tsarin Mulkin Ƙasa. Kuma a dokance bai halasta ba mutum yana Gwamnan Babban Banki ya riƙe wani muƙami, sabod haka sai na rubuta takardar barin aiki. Tun daga wannan lokaci na shiga siyasa”. Zamowarsa Minista Bayan da aka ci zaɓen da ya ɗora Alhaji Shehu Shagari a kan kujerar shugabancin Najeriya, sai shi Shagari ya kira Adamu Chiroma cewa wanne muƙami yake so a cikin gwamnati. Shi kuma sai ya amsa masa da cewa, shi tun farko umarni aka bashi kuma ya bi, saboda haka duk aikin da aka bashi ko na kwasar shara ne zai iya yi. Saboda haka, sai aka yi masa ministan masana’antu (Minister of industry). Bayan shekara biyu kuma aka mayar da shi ma’aikatar gona (Ministry for Agriculture). Bayan sake sabon zaɓe kuma sai aka yi masa Ministan kuɗi (Minister of Finance). Haka nan ma a zamanin mulkin soja na shugaba Abacha ya riƙe ministan aikin gona (Agriculture).

Kafa Jama’iyyar PDP

Bayan an sake mu, wata rana ina Kaduna sai Marigayi Rimi da Sule suka zo suka same ni a Kaduna. Suka ce yanzu an sake sabuwar siyasa, kuma mun zauna a kurkuku mun fahimci juna. Menene abin yi? Sai na ce mu yi siyasar haɗin kai. Daga nan sai Rimi ya kira su Jerry Gana, su Solomon Lar, da sauran yaran ‘Yar’aduwa. Muma sai muka kira abokan siyarmu. Sai muka ce da su to, ga siyasa, sannan kuma abubuwan da aka yi mana na cin mutunci har zuwa lokacin Abacha. Saboda haka mu, bamu yarda soja su dama da mu ba. Mu faɗa mu cewa mu bamu yarda a yi siyasar cutar jama’a ba. Saboda haka sai muka rubutawa Abacha cewa lallai bamu yarda ba sai ya sauka. Bayan faruwar waɗannan abubuwa sai muka kafa PDP. Da muka kafa jama’iyyar ta PDP sai muka ɗebo dukkan tunanin gyara ƙasa, haɗa kai, da kula da jama’a, muka yarada cewa: 1. Najeriya tana buƙatar mutane daga kowane gefe da kowane shahi su haɗa kai; 2. Mutane su girmama juna; 3. Su tabbata cewa sun yi abin da zai haɗa kan ƙasa, saboda an yi juye-juyen mulki duk bai haifar da ɗa mai ido ba. Sannan mun lura cewa lokacin da aka yi juyin mulkin Buhari, duk baki ɗayanmu aka tattara mu aka zuba a ƙiri-ƙiri ba tare da bambacin jamaiyya ba. Saboda haka a nan muka ɗauki darasi da kuma zama da juna. A nan muka fahimci junanmu a sannu, sannan muka zauna lafiya da juna. Kyaututtukan Girmamawa An ƙayatar da marigayi Alhaji Adamu Chiroma da lambar yabo ta ƙasa mai taken CFR, a zamanin shugaba Obasanjo.

Rasuwa

Alhaji Adamu Chiroma, “Ya rasu ne a ranar Alhamis da rana a Abuja, bayan ya sha fama da rashin lafiya. An yi jana'izar marigayi Malam Adamu Ciroma a masallacin Al Noor da ke Abuja. . .


< https://www.rumbunilimi.com.ng/Adamu%20Chiroma.html#gsc.tab=0\>