Ahmed ibrahim zakzaky
An haifi Sayyid Ahmad a ranar Asabar 13th October 1990, wanda yai dai-dai da 24 ga Rabi'ul Auwal 1411. A unguwar kwarbai dake cikin Birnin Zazzau a jihar Kadunan tarayyar Najeriya. Sunan sa Sayyid Ahmad Ibrahim. Yana da Laqubba kadan daka ciki, jama'a na kiran sa *Commander*, Iyayan sa kuma da *Fa'iz* . KARATUN SA. Ya fara da karatun gida ne a bangaran karatun Al-Qur'ani da karatukan Fiqihu da fannin Ibadat da Ma'amalat da kuma fannoni dabam-dabam da ake karantawa a zaurukan karatu a cikin Birnin Zariya, wadannan duk a gun mahaifin sa ya karanta su a gida. Ya yi karatunsa na primary a Buk International School dake daura da filin koyan tuqin Jirgin sama na Aviation dake Zaria, daga shekarar 1996 zuwa 2002 Yayi makarantar Thybow International School Zaria daga 2002 zuwa 2004, daga nan yabari ya koma Zaria Academy daga 2005 zuwa 2007 sai yabar Zaria academy yakoma Holemark har akayi masa double promotion yashiga SS2 maimakon yashiga SS1. Bayan nan yagama Secondary School A 2009, Amma baisamu wucewa makaranta ba sai a 2011. Ya yi amfani da wannan damar wajan fadada bincike a kan wasu fannoni na karatun sa. A lokaci guda kuma ya sami dama sosai wajan taimakon mahaifin Sa a kan ayyuka na yauda kullum da mahaifin sa Shaikh Ibrahim Zakzaky (h) ya saba gudanarwa domin taimakon Al-umma, kamar tafiye-tafiyen sa da ayyukan gine-ginen cibiyoyin addini dama wasu ayyukan dabam. Yasami nasarar wucewa China ne A shekarar 2011, Inda yayi karatunsa na Chemical Engineering wanda a shekarar sa ta qarshe dazai kammala, bayan dawowar sa hutu ne, sojojin gwamnatin ebele jonathan "yan inada kisa suka aiwatar da kisan kiyashi akan masu muzaharar qudus ta duniya a Zaria, wacce ake yi duk shekara, dan nuna tausawa ga al'ummar Palastinawar da haramtacciyar qasar Isra'el keyiwa kisan gilla fiye da shekaru 60+ wanda duniya tai shiru akai. Sayyid Ahmad yana cikin mutum 34 da sojojin suka kashe, ciki har da kannan sa biyu Sayyid Hameed da Sayyid Mahmud. Sayyid Ahmad ya sami cikakkiyar tarbiyya daga mahaifinsa, dan haka ya haifar da ayyuka na musamman da suka zama abin koyi ga yan baya. Tun yana yaro ya yi aiki kafada da kafada fanin tsaro na Harisawan Harkar Musulunci sakamakon cigaban tunanin sa yasa ya kafa rundunar Muassasatu Sayyid Abul Fadalul Abbas (A.S) wannan rundunar bayan kafuwar ta, ta haifar da rassa na fannonin ayyukanta a ciki da wajen harka zuwa sassa dadan-daban. Sayyid Ahmad Yayi shahada a shekarar 2014/25/July. Lokacin yana da shekaru 25 a duniya sojojin Nijeria sum masa kisan irin na gabar jahiliyyar qarnin farko kafin zuwan Manzon Allah (S.A.W.W) ta yanda suka harbi duk wata gaba mafi mushimmanci a jikin sa da harsashi, da dan Adam zai iya dogara da ita dan samun damar motsawa, sun kashe shi tare da dan uwan sa Sayyid Hameed Ibrahim Zakzaky (H) bayan kamun da sukai masu alokacin muzaharar ta Qudus 2014 . . < https://sshahidahmad.simdif.com/nafsun-usman.html\>