Murhu ko Murahu yana daga kayan aikin gida Murhu dai abu ne da ake amfani da shi wajen dafa abinci da sauran girke-girke. Na abinci ne ko na wani abu ne da ake ɗorawa akan murhu. Duk da dai yanzu murhu ya zama tarihi a birni sai dai a ƙauyuka.

Murhu
Bayanai
Ƙaramin ɓangare na stove (en) Fassara
Murhu
murhu
Murhun gargajiya wanda aka sani iyaye da kakanni Akwai murhun duwatsu daake sakawa guda uku akwai Kuma murhun falanke irin Wanda kuma masu sana'an kwale kwale sukeyi Wanda ake zira itace aciki Sannan kuma yanzu Zamani yazoda murhun gawayi Wanda akeyinshi Da wayan dakecikin tayan manyan motoci Bayan ankona tayoyin

Asali gyara sashe

Sannan asali dai ana amfani da duwatsu ne guda uku wajen haɗa murhu, to sai dai yanzun kuma akwai cigaba da aka samu na murhun zamani wanda maƙera suke ƙera shi sai kuma wanda tekanolojin zamani ya kawo kamar wanda ake amfani dashi ta hanyar wutar lantarki da dai sauransu. Wani lokacin akan haɗa duwatsu biyar sai ya zamo murhun tuwo da miya [1]

Hotuna gyara sashe

 
Murhu
 
Murhun ƙarfe na zamani
 
wani ƙaton murhu na yumɓu (na ƙasa)
 
murahun ƙasa
 
murhun gas na zamani

Manazarta gyara sashe

  1. https://hausadictionary.com/murhu