Mukhtar Atiku Kurawa
Mukhtar Atiku Kurawa farfesa ne a fannin ilimin Inorganic Chemistry, masanin ilmin, mai gudanarwa, kuma tsohon Rector watau shugaban makarantar Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kano, Shine shugaban Jami’ar Yusuf Maitama Sule, Kano watau Vice-chancellor.
Mukhtar Atiku Kurawa | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | jihar Kano, 28 ga Augusta, 1970 (54 shekaru) |
Sana'a | |
Sana'a | Malami |
Tarihinsa
gyara sasheAn haifi Mukhtar a ranar 28 ga watan Agusta shekara ta, 1970, a unguwar Kurawa, da ke cikin ƙaramar hukumar Kano, ta jihar Kano. Ya sami PhD a Kimiyyar Inorganic Chemistry a Jami'ar Bristol, United Kingdom U. K a shekara ta, 2005.
Kurawa ya koyar a tsangayar Kimiyya ta Jami'ar Bayero ta Kano, sashen ilmin sunadarai har zuwa lokacin da ya zama Farfesan ilimin Kimiyyar Inorganic Chemistry, a shekarar, 2015.
Manazarta
gyara sashehttps://dailytrust.com/prof-kurawa-assumes-duty-as-new-vc-of-yumsuk.