Muhammadu Gambu
Muhammadu Gambu Shi dai Muhammadu Gambu ya kasance Makadi ne mai fasahar gaske. Kuma wakokinsa cike suke da balaga da azanci da salon magana. Duk da karin harshensa ya yi matukar tasiri cikin wakokinsa amma wannan bai hana manazarta da masu sha’awar wakokinsa fahimta tare da nazartarsu ba.[1][2]
Muhammadu Gambu | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Jega, unknown value |
ƙasa | Najeriya |
Sana'a | |
Sana'a | mawaƙi |
Haihuwa da Iyali
gyara sasheAn haife shi a wajejen shekara ta alif 1949. Mahaifinsa Muhammadu Umar dan Malam Muhammadu Sani dukkanninsu mutanen Fagada ne. Sannan mahaifiyarsa ita ce Malama Zalihatu, sannan abokanan haihuwarta suke limancin garin Laga dake Gwandu. Iyayen Muhammadu Gambu Kambarin Bare-bari ne. Sunan kauyen da yake shi ne Katanga a Ƙaramar Hukumar Maiyama. Kasancewarsa dan Malama, jikan malamai.
Matarsa ta fari Hauwa’u ‘yar garinsu ce Fagada wadda mahaifiyarsa ce ta aura masa ita. Sannan ya kuma auren wata Kulu ta garin Badon hanya a Ƙaramar Hukumar Wammako, sannan ya auri wata Kulun a garin Ambursa. Matarsa ta huɗu ita ce Luba ‘yar Mutanen Maiyama jihar Kebbi. Gambu yana da yara shida maza uku mata uku. Sunansa na gaskiya Muhammadu. Masana suna ganin ya sami lakabin Gambu ne a wajen wakarsa.
Karatu da sana'ar sa
gyara sasheGambu ya tashi gidan ilimi don haka sai da aka saka shi makarantar allo ya budi ido da karatu kafin ya fara kowacce irin sana’a. Ya dan taba noma inda daga bisani ya koma farauta inda yake harbe-harben namun daji. Amma kafin nan ya yi sana’ar alawar suga ya yi sakar tabarma ya yi kirar rariyar tankaɗe ta mata. Ya yi saka da kuma bugi na kamun kifi. Ya yi yawon kokawa da karen mota da yaron mota da sauransu. Yana cikin wannan sana’a ta farauta ne ya dinga haduwa da barayi cikin jeji suna yin hulda. Inda a karshe har ya zama makadinsu. Amma yana taba wakokin masu gari da na ‘yan siyasa.
Gambu bai gaji waka ba ta bangaren uwa ko uba, ya tsinci waka ne sama ta ka ta silar farauta da huldar da ya yi da barayin, sai kuma kasancewarsa dan caca na yankan shakku.
Bunza ya nuna cewa a tsarin fasahar Gambu wakokinsa na sata kari daya suke da shi. Hawa da saukar muryar daya ne sai dai kowane barawo a dora sunansa cikin wakar da irin bayanin da aka yi kansa. Muryarsa ta kidan sata na da dadi sosai. Fasaharsa tsararriya ce, salon hira ya fi yawa a cikin wakarsa. Gambu ya san sata, ya san barayi, ya san kalmomin da ake fitar da sata, a ji su, a gan su.[3].
Mutuwa
gyara sasheGambu ya rasu ranar Laraba 18 ga watan agustan shekarar 2016, ya rasu yana da kimanin shekaru 73 a duniya. Ya bar mata 4 da 'ya' ya da kuma jikoki masu yawa.[4][5].
Manazarta
gyara sashe- ↑ https://hausa.leadership.ng/alhaji-muhammadu-gambu-mai-wakar-barayi-gwarzonmu-na-mako/?amp=1
- ↑ https://aminiya.dailytrust.com/gambu-mai-wakar-barayi-ya-rasu
- ↑ https://www.rfi.fr/ha/najeriya/20141105-gambo-mai-wakar-barayi-ya-tuba
- ↑ https://www.alummarhausa.com.ng/2020/04/tarihin-marigayi-gambu-mai-wakar-barayi.html
- ↑ https://www.bbc.com/hausa/labarai/2016/08/160818_gambu_dead