Muciya: Tana kuma daga cikin kayan aikin gida wadda take cikin dakin girk-girke a koda yaushe. Ana amfani da muciya ne wajen tuka tuwo ko na masara ko shinkafa ko dawa. Kusan dai ko wane irin tuwo da muciya ake tukashi, a lokacin da yayi kuma ya isa a tuƙa tuwon ana gama tuka shi bada jimawa ba sai a kwashe shi a kwano. Mata sune suka fi amfani da ita muciya don su aka sani da harkar girka abinci shiyisa ma sune suka san inda ake ake muciya a kowane gida Muciya mafi yawa ana kuma yinta ne da ice wato sassaka akeyi, sai kuma yanzu akwai ta zamani. [1]

wannan ita ce muciya wadda ake tuka tuwo da ita musamman idan tuwon mai yawa ne, muciya ice kenan

Manazarta gyara sashe

  1. Musa, Aisha (8 May 2018). "Yaro ya bugi ubansa da muciya, uban mai shekara 83 har lahira". legit hausa. Retrieved 14 August 2021.