Sassaka
Sassaƙa na ɗaya daga cikin daɗɗun sana‟o‟in Bahaushe na gargajiya. Wani abin burgewa shi ne, har yanzu akwai masassaƙa a cikin Hausawa. Bugu da ƙari, akwai kayan amfanin Bahaushe da dama waɗanda masassaƙan ne ke samar da su, duk kuwa da sauye- sauyen zamani da aka samu a yau. Ɗaya daga cikin abubuwan da suka fi fice da Bahaushen dauri da na zamani ya dogara kan masassaƙi domin samun sa shi ne “turmi.”
Duk da daɗewa da wannan sana‟a ta yi, mafi yawan Hausawa ba su san matakan da ake bi domi samar da turmi ba, duk da kuwa za a iya cewa a ƙalla akwai turmi guda a gidan kowane Bahaushe. Ba gama- garin Hausawa ba, har cikin manazarta harshe da al‟adun Hausawa, waɗanda suka san matakan sassaƙa ba su da yawa. Yayin da aka nazarci fasahohi da ƙoƙarin masassaƙa, lallai za a tarar cewa sun cancanci a darajanta kayayyakin da suke samarwa. Wannan ne kuma ya sa takardar ta himmatu wajen fito da yadda ake sassaƙa turmi daki-daki tun dagga zaɓen ice, har zuwa tsayar masa da fasali.
Masana da ɗaliban ilimi da dama sun tofa albarkacin bakinsu dangane da ma‟anar sassƙa dai-dai fahimtarsu. A cikin ƙamusun Hausa na CNHN (2006: 393) an bayyana sassaƙa da cewa: “Abin da aka sarrafa daga itace kamar allo da turmi da mutum-mutumi, sana’ar sassaƙa sana’a ce ta samar da surori”.
A ra‟ayin Wushishi (2011: 24) cewa ya yi:
Sana’ar sassaƙa aiki ne na hure ice da aiwatar da shi don a mayar da shi wani abin amfani kamar jirgin ruwa da kujera da kyaure da turmi da taɓarya da akushi da suransu.
Wannan ra‟ayin yana nuni da cewa sassaƙa sana‟a ce ta sarrafa itace. Haka Alhassan da wasu (1982: 54) a cikin nasu littafin suna da ra‟ayin cewa: Sassaƙa na nufin sarar itace da sarrafa itacen ta hure domin aikatar da shi zuwa dukkan abubuwan da ake buƙata.[1]