Monday Anyamaobi Onyezonwu (an haife shi a ranar 27 ga watan Afrilun 1964) lauya ne da ke aiki a matsayin Kwamishinan Ayyuka na Musamman na Jihar Ribas. An rantsar da shi a ranar 18 ga watan Disamban 2015 don maye gurbin Dickson Umunakwe.[1]

Monday Onyezonwu
mutum
Bayanai
Jinsi namiji
Suna Monday (mul) Fassara
Shekarun haihuwa 27 ga Afirilu, 1964
Sana'a Lauya
Ilimi a Jami'ar jihar Riba s
Ɗan bangaren siyasa Rivers State People's Democratic Party (en) Fassara

Rayuwar farko da ilimi

gyara sashe

An haife shi a ƙauyen Umuokewo, ƙaramar hukumar Omuma a jihar Ribas. Ya yi karatun firamare a makarantar jihar Ohim-Oyoro tsakanin shekarar 1970 zuwa 1976. Ya halarci Makarantar Grammar County, Ikwerre – Etche daga shekarar 1976 zuwa 1981. Iliminsa na jami'a ya kasance a Jami'ar Kimiyya da Fasaha ta Jihar Rivers inda ya sami digiri na farko a fannin Shari'a a cikin shekarar 1986. Daga baya ya halarci makarantar koyon aikin lauya ta Najeriya, inda daga nan ya kammala a cikin shekarar 1987.[1]

A matsayinsa na ɗan siyasa, ya riƙe muƙaman siyasa da dama kamar Sakataren rusasshiyar jam’iyyar Social Democratic Party ta Jihar Ribas; Mai ba da shawara kan harkokin shari’a, Majalisar Ƙaramar Hukumar Omuma; Memba, kwamitin riƙo, ƙaramar hukumar Omuma, shugaban matasa, jam'iyyar PDP ta jihar Rivers. Memba, kwamitin gudanarwa na Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya, Uyo kuma Shugaban kwamitin riƙo, ƙaramar hukumar Omuma.[1]

Duba kuma

gyara sashe
  • Jerin mutanen jihar Ribas
  • Gudanar da gaggawa

Manazarta

gyara sashe
  1. 1.0 1.1 1.2 "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2017-03-06. Retrieved 2023-04-10.