Mohammad Afshin Ghadirzadeh
Afshin Kadirzadeh (an haife shi a ranar 22 ga Yuli, 2002) a Bukan, an kira shi mafi guntu mutum a duniya. Kuma ya aje tarihi a cikin kundin Guinness[1]
Mohammad Afshin Ghadirzadeh | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Bukan (en) , 13 ga Yuli, 2002 (22 shekaru) |
ƙasa | Iran |
Sana'a | |
Sana'a | Internet celebrity (en) |
Tsayi | 65.24 cm |
Tarihin rayuwa
gyara sasheAfshin Kadirzadeh[2], matashi dan shekara 20 daga Bokani, tsayinsa ya kai cm 65 , wanda ya kawo masa wasu gazawa.[3] Rashin ilimi da rashin yin wasu ayyuka na yau da kullun da suka shafi rayuwar karkara na daya daga cikin manyan matsalolinsa. Kamar takwarorinsa, wannan matashin yana son ya zauna a bayan makaranta da kuma wurin tattaunawa da malamai da karatu, amma a cewar mahaifinsa, bai je makaranta ba saboda matsalolin jiki da kuma ci gaba da jinya. Duk da Afshin yana da shekara 20 , ga shi kamar yara ‘yan shekara uku. Kuma wannan lamari ya janyo masa fuskantar matsaloli da dama a wannan mataki na rayuwarsa. Wannan dan karamin mutum ne mai budaddiyar hankali da kyawawan dabi’u, shi ya sa ya shahara a wajen mutanen kauyen, kowa ya rika kiransa da sunansa na biyu Muhammad.
Manazarta
gyara sashe- ↑ https://www.guinnessworldrecords.com/news/2022/12/20-year-old-iranian-confirmed-as-worlds-shortest-man-730170
- ↑ https://en.mehrnews.com/news/194986/Iran-s-Afshin-Ghaderzadeh-wins-Guinness-World-Records
- ↑ https://www.ndtv.com/offbeat/watch-irans-afshin-ghaderzadeh-is-crowned-the-worlds-shortest-man-3610680