Miriam Adhikari likita ce kuma masaniya a fannin kimiyya (scientist) kuma ƙwararriya a fannin ilimin likitanci na yara da cututtukan su tare da mai da hankali kan neonatology.[1][2] Ita ce Farfesa Emeritus a Jami'ar KwaZulu-Natal kuma masaniya a fannin ilimin haihuwa a Makarantar Magunguna ta Nelson Mandela.[3] Har ila yau, tana mai da hankali kan ilimin cututtukan yara kuma memba ce a Kwalejin Kimiyya ta Afirka ta Kudu.[4]

Miriam Adhikari
Rayuwa
ƙasa Afirka ta kudu
Karatu
Harsuna Turanci
Sana'a
Sana'a researcher (en) Fassara, likita da scientist (en) Fassara
Employers Jami'ar KwaZulu-Natal
Kyaututtuka

Miriam Adhikari ta ƙwararriya ce a fannin likitanci na yara da cututtuka kuma ta haɗa wallafe-wallafe sama da 100.[5]

Gwamnatin KwaZulu-Natal ta ba ta lambar yabo ta Hidima ta Shekara-shekara a cikin shekarar 2017.[2] Ta ce babban abin da ta fi mayar da hankali a kai shi ne koyawa ma’aikatan jinya mahimmancin kula da iyaye mata da jarirai.[2]

Manazarta

gyara sashe
  1. "Prof. Miriam Adhikari". drill.co.za. Archived from the original on 2017-10-17. Retrieved 2017-10-17.
  2. 2.0 2.1 2.2 "Emeritus Paediatrics Professor Receives Award for Excellence". University of KwaZulu-Natal. 18 January 2017. Retrieved 2017-10-17.
  3. "Professor Miriam Adhikari". clinprac.ukzn.ac.za. Archived from the original on 2019-07-30. Retrieved 2018-07-26.
  4. "Members List « ASSAf – Academy of Science of South Africa". www.assaf.co.za (in Turanci). Archived from the original on 2018-07-26. Retrieved 2017-10-17.
  5. "MIRIAM ADHIKARI | University of KwaZulu-Natal, Durban | ukzn | School of Clinical Medicine". ResearchGate (in Turanci). Retrieved 2020-02-11.