Milka Irene
Milka Irene Soobya ta kasance yar'fim din kasar Uganda ce kuma yar'siyasa wacce ta shahara sanadiyar fitowarta amatsayin Monica acikin shirin NTV Uganda jerin diramomin Deception da kuma Fifi Aripa a Power of Legacy. Ta nemi takarar zama mamba a Majalisar Jinja bayan baiwa Jinja matsayin zama birni a kasar.[1][2]
Milka Irene | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Buwenge (en) , 1989 (34/35 shekaru) |
ƙasa | Uganda |
Karatu | |
Harsuna | Turanci |
Sana'a | |
Sana'a | jarumi |
IMDb | nm9882719 |
Aiki
gyara sasheSoobya ta fara aikin shirin fim ne da fitowa a kananan vidiyoyi na jerin shirye-shirye na kasar Kenya Makutano Junction wanda Philip Luswata ya gabatar da ita, wanda daya ne daga cikin marubutan shirin. Sai dai ta samu shahara asanda ta fito a jagoran mataki Monica a NTV Uganda jerin drama Deception daha 2013 zuwa 2016.[3][4] Daga baya tayi aiki a Akpor Otebele fim din da yayi darekta, The Rungu Girls, Honeymoon is Exaggerated, Christmas in Kampala da kuma Taxi 24. A shekarar 2018, ta fito acikin shirin Power of Legacy amatsayin Fifi Aripa, a freeloader da Rachael's (Tania Shakira Kankindi) babbar kawa.[5]
Siyasa
gyara sasheA 2020, Soobya ta shiga siyasa ka'in dana na'in inda ta nemi zama mamba a Majalisar kasarta don wakiltar Birnin Jinja a karkashin jam'iyyar National Resistance Movement bayan ayyana Jinja amatsayin birni maicin gashin kansa.[6]
Fina-finai
gyara sasheShekara | Film/TV Series | Mataki | Bayanai |
---|---|---|---|
2013 -2016 | Deception" | Monica | Lead role |
2016 | Christmas in Kampala | Christmas film | |
The Rungu Girls | |||
Honeymoon is so Exaggerated | |||
Taxie 24 ug | |||
2016 - to-date | Family Affairs | Herself – Co-host | Talk Show on Spark TV |
2018 | Power of Legacy | Fifi Arripa | Television series, main cast |
Rayuwarta
gyara sasheSoobya an haife ta ne a Jinja daga gidan mahaifin ta Lt. Colonel Samuel Kafude Ngobi da Capt. Namutebi Agnes Mbuga, wadanda dukkanin su sojojin UPDF ne. Ta yi karatun ta a Mbogo High School na O Level, da Mariam High School na A-Level da kuma Jami'ar Kyambogo inda ta kammala da digiri a fannin Procurement and Logistics Management.[7]
Manazarta
gyara sashe- ↑ "Milka on being Monica in 'Deception'". The Independent. Retrieved 26 August 2020.
- ↑ Baike, Prisca. "Deception's Irene Milka tithes faithfully". The Observer. Archived from the original on 2 November 2020. Retrieved 26 August 2020.
- ↑ Batte, Edgar. "Irene Milka: Deception's leading lady". Sqoop. Retrieved 26 August 2020.
- ↑ Male, Marvin. "God's word will bring a turn-around in your life, says actress Irene Milka". Uganda Christian News. Retrieved 26 August 2020.
- ↑ Gachie. "Irene Milka Biography, Music, Family and Awards". Africa Mania. Retrieved 26 August 2020.[permanent dead link]
- ↑ Kazungu, Daniel. "RACE TO 2021 POLLS: Who will be Jinja city's first Women representative?". PML Daily. Retrieved 26 August 2020.
- ↑ "Deception TV Series Star Milka Irene (Monica) Graduates From Campus". Big Eye. Retrieved 26 August 2020.[permanent dead link]