Messaoud Aït Abderrahmane (an haife shi a ranar 6 ga watan Nuwamba a shekarar 1970), tsohon ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne na Aljeriya wanda ya shafe yawancin aikinsa tare da JS Kabylie . Ya kuma buga wa MC Alger da MO Constantine kafin ya yi ritaya. Ya taka leda a matsayin mai tsaron baya na dama da kuma na tsakiya .[1]

Messaoud Aït Abderrahmane
Rayuwa
Haihuwa Mostaganem (en) Fassara, 6 Nuwamba, 1970 (53 shekaru)
ƙasa Aljeriya
Karatu
Harsuna Larabci
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
  JS Kabylie (en) Fassara1989-1995
  Kungiyar Kwallon Kafa ta Aljeriya1990-199350
  Algeria national under-23 football team (en) Fassara1993-199320
MC Alger1995-1996
MO Constantine (en) Fassara1996-1999
 
Muƙami ko ƙwarewa Mai buga baya
Tsayi 177 cm

Ɗan ƙasar Algeria daga shekarar 1990 zuwa 1993, Aït Abderrahmane ya kasance memba na tawagar kasar Algeria da ta lashe gasar cin kofin nahiyar Afirka a shekarar 1990 da kuma gasar cin kofin nahiyar Asiya a 1991 .[2]

Asalin sa gyara sashe

An haife shi a Mostaganem, Aït Abderrahmane ya girma a garin Issers.

Aikin Kulob gyara sashe

Aït Abderrahmane ya fara buga wasa tun yana shekara 12 a kulob din Issers.[3] Yana da shekaru 17, ya shiga cikin matasan matasa na JS Kabylie. Bayan wasanni biyu tare da ƙaramin ƙungiyar, Mahieddine Khalef da Stefan Żywotko suka ɗaukaka shi zuwa babban ƙungiyar.[4] A lokacin da yake tare da JS Kabylie, ya lashe kofuna da dama, musamman gasar cin kofin zakarun nahiyar Afirka na shekarar 1990.[5]

A ƙarshen kakar 1994–95, Aït Abderrahmane ya bar JS Kabylie ya koma MC Alger. Ya shafe kakar wasa guda a can kafin ya koma MO Constantine, inda zai shafe shekaru uku masu zuwa kafin yayi ritaya.[6]

Aikin Kasa gyara sashe

Aït Abderrahmane ya fara taka leda a tawagar kwallon kafar Algeria a gasar cin kofin nahiyar Afirka ta 1990. An saka shi a cikin 'yan wasan farko da za su buga gasar, amma ya janye saboda karatunsa. Koyaya, bayan Rachid Adghigh ya janye saboda rauni, an sake kiran Aït Abderrahmane. A ranar 8 ga Maris, 1990, ya buga wasansa na farko ga ƙungiyar, inda ya fara wasan rukuni na ƙarshe da Masar. Ya buga wasan gaba daya inda Algeria ta ci 2-0. A wasan kusa da na karshe da Senegal, ya fara wasan ne a benci amma an sauya shi a minti na 69, inda ya maye gurbin Kamel Adjas. Ya fara ne a wasan karshe da Najeriya, inda ya buga wasan gaba daya yayin da Aljeriya ta lashe wasan da ci 1-0, inda ta dauki kofin nahiya na farko.[7]

Lamabar yabo a Kulob gyara sashe

https://en.m.wikipedia.org/wiki/Algerian_Ligue_Professionnelle_1 1988–89, 1989–90

https://en.m.wikipedia.org/wiki/CAF_Champions_League 1990

https://en.m.wikipedia.org/wiki/Algerian_Super_Cup 1992

https://en.m.wikipedia.org/wiki/Algerian_Cup 1991–92, 1993–94

Lambar yabo a Kasa gyara sashe

•Africa Cup of Nations: 1990 •Afro-Asian Cup of Nations: 1991 •Mediterranean Games silver medal: 1993

Manazarta gyara sashe

  1. Oukaci, Hakim. "Messaoud Ait Abderrahmane ancien défenseur des Canaris "Jouer à la JSK était mon rêve d'enfance"". La Dépêche de Kabylie (in French). Retrieved April 20, 2012.CS1 maint: unrecognized language (link)
  2. "E.N d'Algérie de Football - Les statistiques de Ait-Abderahmane Messaoud مسعود آيت عبد الرحمان". DZFootball.free.fr. Retrieved April 20, 2012.
  3. http://dzfootball.free.fr/EN/Joueurs/fiche/Ait-Abderahmane-Messaoud.html
  4. https://web.archive.org/web/20120923234143/http://www.dzfoot.com/fiche-1177.php
  5. https://web.archive.org/web/20120923234121/http://www.dzfoot.com/fiche-1175.php
  6. https://web.archive.org/web/20120923234135/http://www.dzfoot.com/fiche-1176.php
  7. http://jskabylie.forumactif.com/t33p45-les-anciennes-gloires-de-la-jsk-itran